Nadin mukamai: Lauya ya shigar da karar Buhari a gaban kotu

Nadin mukamai: Lauya ya shigar da karar Buhari a gaban kotu

Wani lauya mazaunin jihar Legas, Lawarence Nnoli, ya shigar da karar neman babbar kotun tarayya da ke Lagos ta tilasta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kara yawan alkalan kotun koli.

Kasancewar wasu alkalan kotun koli sun yi ritaya kuma har yanzu ba a maye gurbinsu ba, adadin yawan alkalan kotun koli a Najeriya ya ragu zuwa 12 daga 21 da kundin mulki ya ambata.

A cikin takardar karar da ya shigar a gaban kotun, Nnoli ya bayyana cewa rashin nada sauran alkalan "babbar saba doka ne, saboda ya sabawa sashe na 231(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999."

Da ya ke gabatar da hujjojinsa, Nnoli ya bayyana cewa tun watan Oktoba na shekarar 2019 hukumar kula da bangaren sharia (NJC) ta mika sunayen alkalan kotun koli hudu domin a daga darajarsu zuwa alkalan kotun koli.

Nnoli ya yi zargin cewa shugaba Buhari ya yi burus da bukatar NJC saboda har yanzu bai tura sunayen alkalan zuwa majalisar dattijai domin tabbatar dasu ba bayan kusan shekara guda.

Alkalan da NJC ta aika sunayensu sune kamar haka; Adamu Jauro, Emmanuel Agim, C. Oseji, da Helen Ogunwumiju.

Nadin mukamai: Lauya ya shigar da karar Buhari a gaban kotu
Buhari
Asali: Twitter

"Yin hakan sabawa doka ne, kuma tamkar barazana ce ga zaman lafiya da cigaban Najeriya, sannan zai rage karfin gwuiwar da 'yan kasa keda shi wajen samun adalci a kotun koli," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti

Lauyan ya roki kotun ta bayar da wani umarni da zai tilasta shuagaba Buhari yin aikinsa.

Wadanda aka shigar da sunansu cikin takardar kara bayan shugaba Buhari sun hada da; hukumar NJC, alkalin alkalan Najeriya, da shugaban majalisar tarayya.

Duk da kotun daukaka kara ta mika takardar karar mai lamba FHC/C/CS/897 zuwa kotun da Mohammed Liman ke jagoranta, har yanzu ba a saka ranar fara sauraron karar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel