Tone-tone: Tsohuwar MD ta NDDC ta yi ministan Buhari tonon asiri

Tone-tone: Tsohuwar MD ta NDDC ta yi ministan Buhari tonon asiri

Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktar hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC), ta zargi Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta da damfara.

Nunieh ta zanta da manema labarai bayan bayyana da tayi a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa a kan bincikar NDDC.

Akpabio da Nunieh sun bayyana a gaban majalisar ne yayin da ake zargin watanda da N40 biliyan da kwamitin rikon kwarya na NDDC yayi.

A yayin sauraronsu, Akpabio ya ce bai san tsarin ayyukan NDDC ba a zamanin Nunieh saboda ta ki yi mishi bayanin komai.

Amma Nunieh wacce ta jero wasu zarge-zarge a kan Akpabio, ta ce ministan ya tsigeta ne saboda ta ki bashi hadin kai.

Tone-tone: Tsohuwar MD ta NDDC ta yi ministan Buhari tonon asiri
Tone-tone: Tsohuwar MD ta NDDC ta yi ministan Buhari tonon asiri Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ta zargi cewa, Akpabio ya bukaceta da ta canja dalolin da ke asusun bankin NDDC zuwa naira, ta kori shugaban tawagar lauyoyin hukumar wanda dan arewa ne.

Sannan cewa ta cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa tare da yi wa Peter Nwaoboshi sharri.

Kamar yadda Nunieh tace, Akpabio ya ja mata kunne da cewa idan bata aikata abinda yake so ba zai tsigeta.

Ta kara zargin Akpabio da cewa, baya taba sa hannunsa a kan wata takarda sai dai ya sa mukarrabansa su yi damfara.

KU KARANTA KUMA: Zamfara da Sokoto: Sojoji sun ceto mutum 5 tare da ragargaza wasu 'yan bindiga

Ta ce ministan ya bukaceta da ta yi rantsuwar sirri don ya hanata fallasa shi amma ta ki.

"A ranar farko da muka hadu muna hanyar tafiya rantsarwa, ya ce min idan har ban yi abinda yake so ba, zai koreni ba tare da jinkiri ba," tace.

"Ya ce abun farko da zan yi idan na isa Fatakwal shine sauya kudin da ke asusun NDDC daga daloli zuwa naira, Na ji tsoro gaskiya. Bayan haka ya ce in kori Kaltugo ta hanyar sa shi yin murabus na dole saboda dan arewa ne.

"Ya umarceni da in cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa a lokacin Akwagaga, wanda ya gada.

"Ya kawo wata wasika a kan in yi wa Sanata Nwaoboshi sharrin cewa ya karbi kwangilar NDDC. Na ce mishi ba zan iya ba don Nima lauya ce na san hukuncin abinda yake sa ni in yi.

"Akpabio baya taba sa hannu a kan takarda, ba zai sa hannu ba amma zai bukaceni da in yi damfara. Ya so in dauka rantsuwar sirri amma na ki, hakan yasa yace zai cire ni."

Ta kara da cewa Akpabio ya bada kwangila 30 kafin ta zama manajan daraktan hukumar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel