'Ka fara yin murabus kafin mu hadu a kotu'- Da jarida ya mayarwa Osinbajo martani
Jackson Ude, mai kamfanin jaridar 'Poinblank' kuma tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya fara yin murabus kafin ya shigar da kararsa.
A ranar Alhamis ne Osinbajo ya rubuta takardar korafi zuwa ofishin babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Muhammad Adamu, domin neman a binciki ma su alakanta shi da karbar kudi daga hannun Ibrahim Magu.
Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar, ya na fuskantar tuhumar almundahana da barnatar da kudade da kadarorin da EFCC ta kwace.
Kafar yada labarai ta yanar gizo, PointBlank, mallakar Ude ta wallafa rahoton cewa Magu ya barnatar da biliyan N39 tare da bawa Osinbajo biliyan N4 daga cikin kudin a matsayin toshiyar baki.
Rahoton ya yi ikirarin cewa wata majiya ce daga cikin kwamitin binciken Magu ta sanar da jaridar labarin bawa Osinbajo kudin.
"Magu ya sanar da kwamitin bincike cewa ya bawa mataimakin shugaban kasa biliyan N4 bisa umarnin shugaban kasa a ranar da zai bar Najeriya zuwa kasar Ingila domin zaman jinya," a cewar wani bangare na rahoton jaridar Pointblank.
Sai dai, rahoton jaridar bai bayar da cikakken bayani a kan yayin wacce tafiya ne shugaba Buhari ya bayar da umarnin ba, saboda shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila domin a duba lafiyarsa fiye da sau daya.
A cikin wasikar da Osinbajo ya rubutawa IGP ranar Laraba ta hannun lauyansa, Taiwo Osipitan, ya bayyana rahoton a matsayin kage da sharri domin bata ma sa suna, a saboda haka ya bukaci a bi ma sa hakkinsa.
Da ya ke mayar da martani ga Osinbajo, Ude ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa bai kamata mataimakin shugaban kasa ya rubuta takardar korafi zuwa ga rundunra 'yan sanda ba, kamata ya yi ya nufi kotu kawai.
DUBA WANNAN: 'Yan arewa sun yi wa Buhari nunin magajin Magu matukar ya na son ganin aiki da cikawa
"Ba na tsoron Osinbajo da 'yan barandansa. Idan ya na so ya shigar da karata a gaban kotu, akwai bukatar ya fara yin murabus sannan ya shigar da kara.
"Ba zai yiwu a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa ya yi amfani da kudin gwamati domin razana bangaren shari'a ba, sannan ga shi yana da kariya. Osinbajo ya fara yin murabus tukunna," a cewar Ude, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng