PTF: Idan ana samun karin masu COVID-19, ba za mu kore maganar rufe gari ba

PTF: Idan ana samun karin masu COVID-19, ba za mu kore maganar rufe gari ba

A ranar Litinin ne kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19 ya yi magana game da karuwar masu dauke da Coronavirus da ake samu a Najeriya.

Kwamitin ya koka da cewa cutar na kara yawo a kasar, wanda hakan ya na tasiri kai-tsaye wajen sha’anin gudanar da mulki da kuma harkar tsaro.

Shugaban PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana wannan a lokacin da su ka zanta da manema labarai jiya a babban birnin tarayya Abuja.

Boss Mustapha ya ke cewa ba za ayi watsi da yiwuwar sake kawo sabuwar dokar hana fita ba, muddin an samu bukatar yin hakan domin a kare lafiya da ran al'umma.

Mustapha ya ja-kunnen mutane su rika bin dokokin da malaman lafiya su ka gindaya, domin a cewarsa babu ruwan wannan cuta da matsayin mutum.

Jaridar Vanguard ta ce wannan gargadi da gwamnati ta yi ya zo ne a daidai lokacin da gwamnoni uku su ka kamu da muguwar cutar a cikin makon da ya gabata.

KU KARANTA: Shugaban Likitoci ya dauko kwayar cutar COVID-19 wajen duba marasa lafiya

PTF: Idan ana samun karin masu COVID-19, ba za mu kore maganar rufe gari ba
Boss Mustapha
Asali: UGC

COVID-19 ta harbi David Umahi na Ebonyi, Ifeanyi Okowa na Delta da takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, wanda shi tuni ya warke.

“A kwanakin bayan nan mun samu karuwar wadanda ke dauke da kwayar cutar COVID-19, musamman a cikin manyan mutane masu mulki.” Inji Boss Mustapha.

“Wannan ya na da tasiri kai-tsaye ga gudanar da mulki da tsaron kasarmu. Mu na kira ga gaba daya mutane su kara ta-ka-tsan-tsan. Wannan kwayar cuta ba ta kula da mukamin mutum.”

Ya ce: “Idan abin ya yi kamari, in ta kama za mu bada shawarar a rufe gari. Za mu fadawa shugaban kasa, shi zai duba lamarin, ya dauki mataki bayan shawarar da mu ka bada.”

Shugaban wannan kwamiti ya ce PTF za su cigaba da aika sakonni domin wayar da kan jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel