Saurayi ya kashe budurwarsa ya jefa gawarta rijiya sboda ta ki amincewa da shi lokacin da a ziyarci gidansa

Saurayi ya kashe budurwarsa ya jefa gawarta rijiya sboda ta ki amincewa da shi lokacin da a ziyarci gidansa

Wani saurayi da ake zargi da aikata laifin kisan kai ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa, Happiness Winfred, mai shekaru 30, tare da jefa gawarta a rijiya.

Saurayin, Shagbada Erigga, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da aka yi bajakolinsa tare da wasu sauran ma su laifi 32 a hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar Oyo da ke unguwar Eleyele a garin Ibadan.

Erigga ya bayyna cewa ya kaiwa Happiness farmki ne saboda ta ki amincewa da shi lokacin da ta ziyace shi a gidansa.

Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da marigayiyar ta ziyarce shi a gidansa da ke yankin Oritoke a unguwar Ojoo a garin Ibadan.

"Ta zo gidana da misalin karfe 7:00 na ymmacin ranar Lahadi, na nemeta bayan mun yi wanka amma sai ta ki amincewa, har hakan ta kai ga mun samu sabani.

"Na tambayeta dalilin da yasa sai na roketa koda yaushe kafin ta amince da ni, na mareta, ita ma ta rama.

"Ta fadi kasa jini na zuba daga bakinta bayan na nausheta sau uku a makogoro. Na dauki gawarta na jefa a cikin rijiya bayan ta mutu.

Saurayi ya kashe budurwarsa ya jefa gawarta rijiya sboda ta ki amincewa da shi lokacin da a ziyarci gidansa
Shabagda Erigga
Asali: Twitter

"Asirina ya tonu ne bayan daya daga cikin makwabtana ya zo diban ruwa a rijiyar bayan dawowarsa daga aiki.

DUBA WANNAN: Magu ya bayyana kasar Afrika da mabarnata dukiyar Najeriya suka mayar gida

"Makwabcina ya fahimci ruwan rijiyar ya gurbace, ya sauya launi kuma ya na wari. Daga bisani sun gano cewa akwai gawar mutum a cikin rijiyar.

"An kama ni bayan sun kai rahoto ofishin rundunar 'yan sanda," kamar yadda mai laifin ya sanar da manema labarai.

Rundunar 'yan sanda ta ce an samu kayan laifi a tare da Erigga da suka hada da wayar salula, agogon hannu, sarka, jakar hannu, takalmi, da sauran wasu kaya mallakar marigayiya Happiness.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng