Jam'iyyar APC ta yi martani a kan sauya shekar Obaseki

Jam'iyyar APC ta yi martani a kan sauya shekar Obaseki

A ranar Juma'a 19 ga watan Yunin 2020 jam'iyyar APC tace gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya barta tun kwanaki kadan da suka gabata.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya sanar da hakan a wata hirar waya da aka yi da shi a garin Abuja.

A martanin da yayi a kan labarin sauya shekar Obaseki zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce tuni gwamnan ya bar jam'iyyar APC.

Issa-Onilu ya ce, "Babu mamaki a wannan al'amarin. Mun san zai sauya sheka tuntuni tunda ya bar jam'iyyar APC. Don haka babu abun mamaki."

Jam'iyyar APC ta ce Obaseki ya bai cancanci tsayawa takarar zaben fidda gwani ba saboda banbance-banbance a takardunsa.

Ya bar jam'iyyar APC kuma ya bayyana cewa zai bayyana madakatarsa a cikin kwanaki kadan.

Gwamnan jihar Edo samu ganawa da gwamnonin PDP tare da wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Amma a yau Juma'a, Gwamnan ya bayyana komawarsa jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Jam'iyyar APC ta yi martani a kan sauya shekar Obaseki
Jam'iyyar APC ta yi martani a kan sauya shekar Obaseki. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamna a Edo a APC

A wani labari na daban, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na shiyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya nesanta kansa daga sabon umurnin da kotu ta bayar da umurtar shi ya kama aiki a matsayin sakataren jamiyyar na kasa.

Salihu ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa ba zai yi wu ya bi umurnin ba saboda ya saba matakin da jam'iyyar ta dauka yayin taron shiyoyi da aka gudanar inda aka nada Waziri a matsayin sakaren jam'iyyar na kasa.

Sallihu ya ce, "Shiyya ta, Arewa maso Gabas ta zabi Waziri Bulama a matsayin mukadashin sakatare a gaban shugaban Majalisar Dattijai, gwamnonin APC da wasu masu ruwa da tsaki.

"Ina wurin taron a lokacin da aka dauki wannan matakin. Saboda haka mene zai sa in koma in bi umurnin kotu na kama aiki a matsayin sakataren jam'iyya na kasa?

"Ba da ni za ayi wannan tabargazan ba. Ba hali ne bane yin irin wannan mumunan siyasar kuma na yi tir da wadanda suka aikata wannan abin.

"A irin wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da wata babban kalubale, kamata ya yi duk masu kaunar jam'iyya su hada kai wuri guda don tafiyar da jam'iyyar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel