An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'

An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'

Wata babbar kotun sojoji da ke zamanta a Abuja ta zartar da hukunci a kan tsohon kwamandan rundar sojojin jihar Sokoto, Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki, bayan an gurfanar da shi a gabanta bisa tuhumarsa da laifin satar kudin rundunar soji.

Kotun ta sanar da cewa ta samu hannun Janar Otiki a cikin dukkan tuhuma biyar da aka gurfanar da shi a gabanta dasu.

A saboda haka, kotun ta sanar da cewa ta zartar da hukuncin korar Janar Otiki daga aiki 'babu girma, babu arziki'.

A cewar kotun, wacce ke karkashin Laftanal Janar Lamidi Adeosun, ta samu Otiki da laifin rashin da'a da biyayya ga dokokin aikin rundunar soji tare da samunsa da aifin sata da karkatar da kadarar gwamnati da sauran wasu laifukan.

Duk da an kore shi daga aiki, kotun ta sanar da cewa an rage masa matsayi zuwa birgediya janar.

Hukuncin zai fara aiki bayan kwamitin koli na rundunar soji ya rattaba hannu a kansa.

An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'
Janar Otiki a gaban kotun rundunar sojoji
Asali: UGC

Kotun ta bukaci kwamitin bincike na musamman da aka kafa ya mayar da miliyan N135.8 da aka samu a wurin janar Otiki zuwa asusun rundunar soji.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun kaiwa sojoji hari, sun kashe 24

Kazalika, rundunar soji ta bukaci a mallaka mata wata miliyan N150 da aka gano janar Otiki ya mallaka, kuma ya kasa bayyana tushensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel