Yanzu-yanzu: Bayan musayar wuta, dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram

Yanzu-yanzu: Bayan musayar wuta, dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram

'Yan bindigar da ake zargin mayakan ta'addancin Boko Haram ne a halin yanzu sun kai hari kananan hukumomi biyu na jihar Borno a lokaci daya, majiyar jami'an tsaro ta sanar.

Mayakan ta'addancin sun tsinkayi garin Monguno wurin karfe 11:30 inda suke ta harbe-harbe ta ko ina.

Kamar yadda majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar, ana musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da dakarun sojin Najeriya.

Ma'aikacin NGO ya sanar da jaridar Daily Trust cewa harbe- harben bindiga da kararta ne yake ta tashi ta ko ina.

"A halin yanzu da muke magana, mayakan suna nan a Monguno, ana ta jin tashin karar bindiga. Dakarun soji na ragargazarsu. Ba mu da kwanciyar hankali, ku yi mana addu'a," yace.

Hakazalika, 'yan ta'adddan sun kai hari a wani kauye mai suna Usmanati Goni da ke karamar hukumar Nganzai a sa'o'in farko na ranar Asabar.

Kamar yadda wani mafarauci ya sanar, maharan sun bayyana wurin karfe 10 na safe inda suka fara harbin farar hula.

Har a halin yanzu ba a san yawan jama'ar da aka kashe ba a yayin rubuta wannan rahoton.

Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram na ragargaza kauyuka biyu a Borno
Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram na ragargaza kauyuka biyu a Borno
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Rikici tsakanin dan uwan Buhari da Aisha Buhari: An ji harbin bindiga a Aso Rock

Rundunar sojin Najeriya ta fatattaki mayakan ISWAP a garin Monguno da ke jihar Borno ta yankin arewa maso gabas din kasar nan.

Jami'an tsaro da mayakan sun yi musayar wuta bayan da 'yan ta'addan suka kutsa garin a ranar Asabar tare da fara harbe-harbe.

Dubban 'yan gudun hijira da ke garin sun fara tserewa don neman mafaka.

Channels TV ta gano cewa, mayakan sun kai hari garin Nganzai da Gubio a lokaci daya duk da ba a samu rashin rayuka ba.

Harin ya zo ne bayan da annobar korona ke hauhawa a jihar Borno. A ranar Juma'a, an gano cewa mutum 42 sun sake kamuwasa cutar, kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bayyana.

A halin yanzu, jihar Borno ce ke da mafi yawan masu cutar a yankin arewa maso gabas inda ta tabbatar da kamuwar mutum 423 da mutuwar mutum 26.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel