'Yan sanda sun kama wani dan kasuwa da ke lalata kananan yara almajirai

'Yan sanda sun kama wani dan kasuwa da ke lalata kananan yara almajirai

Rundunar 'yan sanda a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, ta kama wasu mutane goma da ke aikata laifin luwadi da kananan yara maza, yawancinsu almajirai.

Daga cikin mutanen da aka kama akwai wani babban dan kasuwa a garin Jalingo.

Da yake tabbatar da kama mutanen, kakakin rundunar 'yan sandar jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce zasu gurfanar da mutanen da zarar an kammala bincike a kansu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa 'yan bijilanti ne suka fara kama wani mai suna Umar Isa yana lalata da wani karamin yaro mai shekaru 10 a wani kango a Jalingo.

Kama mutumin ne ya kai ga kama sauran 'yan tawagar masu lalata yaran da suka hada da babban kasuwar.

Rundunar 'yan sanda ta gano cewa masu laifin sun hada wata kungiya ta masu lalata yara maza, yawancinsu almajirai.

Masu laifin sun saka kananan yara da yawa a cikin mummunan dabi'ar luwadi, kamar yadda rundunar 'yan sanda ta bankado.

'Yan sanda sun kama wani dan kasuwa da ke lalata kananan yara almajirai
Almajirai
Asali: UGC

A ranae Alhamis ne kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, ta amince da saka dokar ta baci a kan fyade, cin zarafin mata da kananan yara a Najeriya.

Gwamnonin sun sake jaddada anniyarsu na ganin cewa dukkan wadanda aka samu da aikata wannan laifi sun fuskanci hukuncin da ya dace da su.

DUBA WANNAN: Ba fansho, ba garatuti: An kori Janar a rundunar soji saboda sukar shugaban kasa

Hakan na cikin sakon bayan taro ne mai dauke da sa hannun shugaban NGF, Dr Kayode Fayemi bayan taro karo na 10 da kungiyar ta yi a kan COVID-19 ta intanet a ranar Laraba.

An fitar da sakon bayan taron ne a Abuja a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnonin sunyi tir da dukkan wani nau'i na cin zarafin mata da yara kanana, inda suka dauki aniyar ganin an hukunta wadanda aka samu da laifin.

"Ana kira ga gwamnonin da ba su riga sun amince da fara amfani da dokar hana cin zarafin mata da yara ba su gaggauta yin hakan tare da dokar da aka yi wa kwaskwarima na ganin an gurfanar da wadanda aka samu da laifin cikin gaggawa.

"Har wa yau dokar ta tanadi bude rajista na mutanen da aka samu da laifin yin fyade a kowanne jiha domin yi musu fallasa da kunyata su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel