'Ya na da Kirki': Tsohon Gwamna Ya Fadi Kyautar da Marigayi Fafaroma Ta Taba ba Shi
- Tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Fafaroma Francis, wanda ya cika a ranar Litinin
- Obiano ya ce sun gana da Fafaroma a Vatican a 2020, inda ya karɓi lambar Papal Knighthood, yana nuna farin ciki da ganawar
- Ya ce Fafaroma ya nuna kirki da sadaukarwa, ya ba su kyaututtuka ciki har da hularsa ta zucchetto, alamar saukin kai da daraja
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - A cikin wata sanarwa ta musamman, tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya bayyana jimamin rasuwar Fafaroma Francis.
Fafaroman ya rasu ne a ranar Litinin da ake bikin Easter, bayan ya kamu da cuta, lamarin da ya girgiza duniya baki ɗaya.

Asali: Facebook
Tsohon gwamna ya hadu da Fafaroma Francis
Willie Obiano, a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce Fafaroma mutum ne mai girman ruhaniya, amma mai sauƙin kai da nutsuwa a hulɗarsa da mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ya gana da marigayi Fafaroma Francis a Vatican a ranar 15 ga Janairu, 2020, lokacin da aka ba shi lambar girma ta Papal Knighthood.
Obiano, wanda ke da matsayin 'Knight Commander' na 'Papal Order of St. Gregory', ya bayyana ganawar da cewa ta kasance abin ban mamaki.
"Na yi tsammanin zai kasance mutum mai nesa-nesa da mutane, amma sai na same shi da sauƙin kai, ga kuma kirki."
- Willie Obiano.
Yaron Obiano ya dauki hoto da Fafaroma
Tsohon gwamnan ya ce sun zauna da iyalinsa a Domus Sanctae Marthae, inda Fafaroma Francis ke zaune maimakon fadar Vatican.
Obiano ya bayyana wani lokaci na musamman da ɗansa, Chukwudifu, ya ɗauki hoto da Fafaroma cikin farin ciki.
Ya ce wannan abin da Chukwudifu ya yi, zai iya zama abin suka ga wasu saboda girman Francis, amma Fafaroman ya yi murmushi, ya kuma yarda da daukar hoton.
Ya kara da cewa wannan hali na Fafaroman ya nuna yadda yake tafiyar da rayuwarsa da karantarwarsa cikin sauki da gaskiya.

Asali: Facebook
Fafaroma ya yi wa tsohon gwamnan kyauta
Obiano ya ce Fafaroma ya ba su kyaututtuka, ciki har da zobuna masu tsarki ga matarsa Ebelechukwu da ‘yarsa Dr. Gechi.
Ya ce shi kansa ya karɓi hular Fafaroma, da ake kira da 'zucchetto', wadda ta kasance hular al’ada a tarihin wannan mukami.
Ya ce ya ajiye hular cikin gilashi na musamman a dakin da ya ke gudanar da ibadunsa domin tuna halin tawali’u da mutuntaka na Fafaroma.
Obiano ya bayyana Fafaroman da cewa mutum ne mai sauƙin kai da sauƙin magana kamar wanda suka jima da sanin juna.
Me zai faru bayan mutuwar Fafaroma Francis?
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Fafaroma Francis ya rasu yana da shekaru 88, bayan shekara 12 yana jan ragamar cocin Katolika mai mabiya sama da biliyan 1.4 a duniya.
Mutuwarsa ta haifar da fara aiwatar da tsarin zaɓen sabon Fafaroma, wanda aka gada tun daɗewa, kuma manyan jami’ai 138 ke jagoranta.
A wannan rahoto, Legit Hausa ta bayyana yadda ake gudanar da zaɓen Fafaroma, su waye ke da damar kaɗa kuri’a, da wanda ya cancanci zama jagora.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng