Buhari da El-Rufa'i sun kebe a fadar shugaban kasa

Buhari da El-Rufa'i sun kebe a fadar shugaban kasa

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, wanda ya ziyarce shi a fadarsa da ke Asorock a Abuja.

Duk da ba a bayyana dalilin ganawarsu ba, Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa, ya ce shugabannin biyu sun kebe a fadar shugaban kasa.

A ranar Talata ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sassauta tsauraran dokokin da ya kafa don dakile annobar korona a jihar.

Kamar yadda gwamnan ya sanar ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2020, ya ce manyan shaguna za su iya komawa bakin sana'o'insu.

Masallatan Juma'a da Majami'u za su iya budewa a ranakun Juma'a da Lahadi kadai, amma karkashin kiyaye dokoki.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa, masu sana'ar aski da wuraren wanke kai duk za su iya budewa.

Otal za su iya budewa tare da wuraren cin abinci da kuma mashaya. Wuraren cin abincin za su iya budewa ne bayan an yi musu feshin kashe kwayoyin cuta.

Buhari da El-Rufa'i sun kebe a fadar shugaban kasa
Buhari da El-Rufa'i
Asali: Twitter

Hakazalika, Gwamnan ya bayyana cewa babu yuwuwar bude makarantu da kasuwanni.

"Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samun matsaya a kan lokacin da ya kamata a bude kasuwanni ka makarantu," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Hanyar Abuja: 'Yan bindiga sun kashe direbobi biyu, sun yi awon gaba da fasinja 16

"Shugaban ma'aikatan jihar zai sanar da lokacin da ya kamata ma'aikata su koma bakin aikinsu," gwamnan ya kara da cewa.

Gwamna Nasir El-Rufai ya shawarci jama'ar jihar da su bada goyon baya wajen dakile yaduwar annobar a jihar.

"Kamar yadda muka jure dokar hana walwala ta makonni goma, mu koma neman na kanmu ba tare da taimakawa yaduwar cutar ba.

"Mu nuna cewa za mu iya zama lafiya duk da sassaucin dokar," a cewar El-Rufai.

Makonni goma kenan da gwamnan ya sanar da rufe jihar tare da saka dokar hana walwala a cikinta tun bayan da ya kamu da muguwar annobar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel