Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria

Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria

Wata matar aure, Hauwa'u Sulaiman, wacce ke zaune a gida mai lamba 70 a unguwar Alfadarai da ke Zaria, ta haifi 'yan hudu a babban asibitin Gambo Sawaba da ke garin Zaria.

Kafin haihuwar 'yan hudun a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, Hauwa'u ta haifi yara 13 a baya.

Yayin hirarta da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata, Hauwa'u ta ce yanzu tana da 'ya'ya 17 daga haihuwa takwas da ta taba yi.

An mayar da Hauwa'u da jariranta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zaria domin samun kyakyawar kulawa.

Hauwa'u ta ce jariri daya namiji daga cikin 'yan hudun da ta haifa ya mutu kafin su karasa asibitin ABUTH

Ta ce ragowar jarirai uku na bangare na musamman domin kulawa da kananan yara a yayin da ita kuma take samun kulawa a bangaren karbar haihuwa na asibitin.

Ta kara da cewa sai da aka kara mata jini leda biyu yayin da take haifar jariran.

Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria
Uwar 'ya'ya 13 ta haifi 'yan hudu a Zaria
Asali: UGC

"Ina cikin koshin lafiya da karfin jiki, amma ma'aikatan lafiya sun bani shawarar na cigaba da hutawa a asibiti domin su saka ido a kaina kafin su sallameni," a cewar Hauwa'u.

Mijin Hauwa'u, Sulaiman Mohammed, ya ce matar tasa ta taba haihuwar 'yan uku har sau biyu, tagwaye sau biyu, da kuma haihuwar dai - dai sau uku, a baya kafin ta haifi 'yan hudu yanzu.

Sulaiman, mai sana'ar tukin mota, ya ce dan uwansa ya ke taimaka masa a kan harkar yaransa duk lokacin da bukata ta taso.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Sanusi II zai fuskanci tuhumar badakalar biliyan N2.2 a gaban kotu

Kazalika, Saudatu Haruna, mahaifiyar Sulaiman ta ce bata yi mamakin cewar Hauwa'u ta haifi 'yan hudu ba.

Ta alakanta abin da gado tare da bayyana cewa sau uku tana haifar tagwaye a lokuta daban - daban.

Saudatu ta kara da cewa a cikin 'yan uku aka haifi mahaifiyarta, sannan mahaifinta tagwaye ne, a saboda haka haihuwa 'yan hudu a zuri'arta ba zai zama abin mamaki ba.

Dakta Isa Abdulkadir, babban likita a bangaren yara a asibitin ABUTH, ya ce ragowar jariran uku suna cikin koshin lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel