Sanusi II zai fuskanci tuhumar badakalar biliyan N2.2 a gaban kotu

Sanusi II zai fuskanci tuhumar badakalar biliyan N2.2 a gaban kotu

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta amince da bukatar hukumar sauraron korafi da yaki da cin hanci ta jihar Kano (KSCACC) a kan biciken tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, bisa zarginsa da badakalar sayar da kadarorin fadar Kano.

A cikin watan Maris ne hukumar KSCACC ta fara biciken Sanusi II a kan zarginsa da badakar kudaden da yawansu ya kai biliyan N2.2.

Ana zargin cewa Sanusi II ya karbi kudaden bayan ya sayar da wasu kadarorin fadar masarautar Kano.

KSCACC tana zargin Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), da laifin sayar da wasu filayen fadar masarautar Kano da ke Darmanawa, Hotoro da Bubbugaje.

Tsohon sarkin ya garzaya kotu domin neman ta dakatar da KSCACC daga gayyatarsa tare da bincikarsa a kan zargin.

A ranar Talata ne mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ta yi watsi da bukatar Sansi tare da bayyana cewa hukumar KSCACC da shugabanta na da ikon tuhumarsa a kan zargin da suke yi masa, saboda doka ta basu dama.

A cewar hukumar KSCACC, tsohon sarki Sanusi II, ya sayar da wani fili mai lambar mallaka: CON-RES-2016-503, ga wani kamfani mai suna 'Family Fund Limited' a cinikin da babu hannu kowa sai mutane uku; Shehu Dankadai (Sarkin Shanu), Sarki Ibrahim (Makaman Kano) da Mustapha Yahaya (Dan Isan Lapai).

Sanusi II zai fuskanci tuhumar badakalar biliyan N2.2 a gaban kotu
Sanusi II
Asali: Twitter

Sanusi II ya samu matsala da gwamnan jihar Kano, Dakta Andullahi Umar Ganduje, a lokacin da yake kan karagar Sarkin Kano.

DUBA WANNAN: Zanga - zanga ta barke a Katsina a kan rashin tsaro, an kone allon kamfen din Buhari da Masari (Hotuna)

Tun a shekarar 2017 gwamnatin Kano ta fara binciken masarautar Kano a karkashin Sansui II da laifin tafka badakala.

Majalisar jihar Kano ce ta shiga maganar har aka janye batun binciken bayan wasu manyan mutane sun shiga lamarin.

A shekarar 2019 ne Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar Kano, lamarin da wasu ke ganin an yi da gangan domin rage karfin Sanusi II a lokacin da yake mulkin masarautar Kano.

Bayan dangantaka ta cigaba da tabarbarewa, gwamnatin Kano a karkashin Ganduje ta tsige Sanusi II daga kan karagar Sarkin Kano a ranar 9 ga watan Maris, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel