Ban yarda da cutar korona ba, babu abunda za ta iya yi mani – Gudaji Kazaure

Ban yarda da cutar korona ba, babu abunda za ta iya yi mani – Gudaji Kazaure

Dan Majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana matsayarsa a kan annobar coronavirus wacce ta addabi kasar.

Gudaji ya ce koda dai baya karyata batun wanzuwar cutar amma dai shi bai yarda korona za ta iya yi masa komai ba.

Ya ce Allah ne ke saukar da annoba kuma shine yake yaye wa bawansa.

Har ila yau dan majalisar ya nuna rashin jin dadi kan yadda aka bai wa cutar korona muhimmanci a kasar alhalin yan bindiga na barnar da ta fi ta korona.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A hira da ya yi da shashin Hausa na BBC, an jiyo dan majalisar na fadin:

Ka fahimci maganata, ai ni nace ba jama’ a ba. Ni nace, na danganta abun da kaina ne. Kuma abunda nake so ka gane ba nace cutar korona karya ce ko babu ita ba.

Ni nace, ni Muhammadu ni babu abunda cutar korona za ta yi mani saboda abunda na yarda dashi shine, cuta Allah ne ke saukar da ita kuma shine yake dauke wa bawansa.

Sannan yarda da kaddara, idan ka yarda da kaddara, ba za ka yarda wani ko wata cuta na iya cutar da kai ba.

Abunda yasa kuma nake so mutane su gane, mutum nawa korona ta kama ta kashe a jihar Kano? mutum nawa rashin lafiya ta kashe? Mutum nawa bandit suka kashe a tsakanin Sokoto da Zamfara da Katsina?

Ka duba ka ga yadda cutar nan aka bata muhimmanci a kowace jiha ko wace karamar hukuma a Najeriya aka fidda makudan kudi, amma mutum nawa ta kashe?

A baya mun ji cewa Gudaji ya yi magana a kan hanyar da yake bi da kudinsa da yake samu a majalisar wakilai ta tarayyar kasar.

Gudaji ya jadadda cewa baya ga alawus da albashinsa babu wani kudi na daban da ake bashi a matsayinsa na dan majalisa.

Ya kuma bayyana cewa albashinsa kwata-kwata baya wuce masa kwana goma, domin a cewarsa yana karar da kudin ne wajen taimaka wa al’ummarsa. Ya ce duk wata a kalla ya kan taimaka wa mutum 200 zuwa 300.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel