COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar

COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar

Wani kwararre a fannin tsari da shugabanci, Dr. Tunji Ogunyemi, ya ce a kalla jihohi 32 ne za su kasa biyan albashi bayan annobar korona ta wuce.

Ya ce akwai yuwuwar a sake duba kasafin kudin Najeriya bayan wannan zabtarewar da aka yi sakamakon abinda ke faruwa a fadin duniya.

Masanin tattalin arzikin kuma lauya wanda yake mukaddashin shugaban sashen karantar tarihi na jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, ya yi kira ga gwamnati da ta hadu da shugabannin kwadago don kara duba takardar da kwamitin Kwamared Hassan Sunmonu ya fitar.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya ce jihar za ta fuskanci babban kalubale bayan annobar korona ta tafi, jaridar The Nation ta ruwaito.

COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar
COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ogunyemi, wanda ya tattauna da wani gidan rediyo da ke Osogbo, ya ce: "Gwamnatin tarayya za ta iya hanzarta wa wurin buga kudade don biyan ma'aikata ba sai ta jira sun samu ta wani wuri ba.

"Amma babu jihar da za ta iya yin haka. Tuni jihohi ne suka zabtare kasafin kudin su saboda raguwar tallafi daga gwamnatin tarayya.

"Abinda jihohi za su samu a watan Yuni zai zama rabin wanda aka samu a watan Janairu. Jihohi hudu ne kacal za su samu daidaito.

"Damar da ma'aikatan gwamnati suke da ita yanzu shine babu wanda zai ce su tafi ba zai biya ba. Amma jihohi za su iya zabtare albashinsu saboda ba za su iya biya ba. Za su iya biyan ma'aikata ne da abinda suke da shi.

"A halin yanzu, jihohi irin su Kaduna, Delta, Filato, Taraba da Gombe duk sun zabtare albashin ma'aikatan su."

KU KARANTA KUMA: Za mu fara sallaman masu cutar Korona daga asibiti ko da basu warke ba - NCDC

Ya kara da cewa, "Babban kalubale ne ke tunkarar mu kai tsaye, sai mun kwashe shekaru biyar a jere kafin mu koma daidai."

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kamfanin man fetur ta kasa (NNPC) ta ce ta samar da manhajar zakulo wadanda suka yi ma'amala da masu cutar korona wacce za a iya amfani da ita a sassa daban-daban na fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel