Hotunan sashen filin jirgin sama na Kano da gwamnatin Buhari ta zamanantar
Gwamnatin tarayya ta kammala sabunta tare da zamanantar da sashen saukar jiragen kasa da kasa a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.
Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da cewa an kammala aikin zamanantar da bangaren filin jirgin saman kamar yadda aka kammala na Abuja da Fatakwal.
A cewar Bashir Ahmad, yanzu haka gwamnatin shugaba Buhari ta na cigaba da aikin zamanantar da filayen tashi da saukar jiragen sama na jihohin Legas da Enugu.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa ranar Asabar, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce kusan dala biliyan daya ce aka sace wa Najeriya karkashin salon mulkin soji a Najeriya.
A wata takarda da aka wallafa a Newsweek, shugaban kasar ya jinjinawa kasashen da suka dawo da kudin.
Duk da Buhari bai kira sunan Sani Abacha ba kai tsaye, amma a bayyane take cewa yana magana a kan mulkin soji na tsakanin 1993 zuwa 1998.
DUBA WANNAN: Barden yakin kungiyar Boko Haram, Saad Karami, ya mika wuya ga rundunar soji
Takardar shugaban kasar ta zo ne bayan makonni uku da kasar nan ta samu dala miliyan 311 daga Amurka.
Kafin hakan, kasar Najeriya ta karbi wasu kudaden daga kasashen Amurka da Switzerland.
Bayan Najeriya ta sake samun wadannan kudi daga Amurka da Bailiwick, Abubakar Malami, Antoni Janar din tarayya ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen kammala babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, hanyar Abuja zuwa Kano da kuma babbar gada ta biyu ta Niger.
A takardar, Buhari ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen yin samar da kayan more rayuwa ga 'yan Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng