Ba zan lamunta ba - Shugaban kasa ya ja kunnen ƴaƴansa game da yi ma dokar hana fita karan tsaye

Ba zan lamunta ba - Shugaban kasa ya ja kunnen ƴaƴansa game da yi ma dokar hana fita karan tsaye

Shugaban kasar Kenya, Mista Uhuru Kenyatta ya gargadi ƴaƴansa musamman maza daga cikinsu dangane da yi ma dokar da ya sanya ta hana fita karan tsaye.

Shugaba Kenyatta ya sanya dokar hana fita a kasar ne domin dakile yaduwar annobar Coronavirus, inda a yanzu haka cutar ta fi kamari a birnin Mombassa ta kasar.

KU KARANTA: Mutane 5 sun mutu, 5 sun jikkata a wani hadari da ya faru a jahar Kano

Sai dai da kansa Kenyatta ya bayyana ma jama’an kasar cewa a kwanakin baya yaransa biyu sun karya wannan doka, inda suka yi takanas ta Kano zuwa birnin Mombassa don holewa.

Kazalika shugaban ya nuna damuwarsa da yadda yaran nasa suka jefa rayuwar mahaifiyarsa, kakarsu kenan, Ngina Kenyatta cikin hadarin kamuwa da cutar saboda a wurin ta suka sauka.

Iyalai da mahaifiyar Kenyatta suna zama ne a Mombassa, guda daga cikin yankunan hudu na kasar da gwamnati ta sanya dokar takaita zirga zirga, inji rahoton BBC Hausa.

Ba zan lamunta ba - Shugaban kasa ya ja kunnen ƴaƴansa game da yi ma dokar hana fita karan tsaye
Uhuru Kenyatta Hoto BBC
Asali: UGC

Shugaban ya jaddada cewa dokar hana fita don yaki da annobar Coronavirus na kan kowa, hatta iyalansa sai sun yi biyayya ga wannan dokar don kare lafiyarsu da lafiyar sauran jama’a.

Sai dai al’ummar kasar Kenya sun caccaki Kenyatta saboda rashin daukan tsauraran matakai a kan yaran nasa da ya tabbatar sun karya dokar, kamar yadda ake yi ma kowa.

Hukuncin wanda aka kama ye keta dokar hana fita a Kenya shi ne a mika shi cibiyar killacewa, har sai ya dauki wasu yan kwanaki an tabbatar da bai kamu da cutar ba, sa’annan a sake shi.

Amma sai ga shi yaran shugaban kasa sun karya dokar, ya tabbatar sun karyata, amma ba’a mika su ga cibiyar killace wadanda ake zargi da kamuwa da cutar ba.

A wani labari kuma, Wasu masoya biyu yan kasar Kenya sun gano cewa ashe babansu daya bayan sun dauki tsawon lokaci suna soyayya da juna, har an sanya musu ranar aure.

Jaridar The Nation ta ruwaito a bisa dole ta sa John Njoroge ya kashe aurensa da Rose Wanjiku kasantuwar sun gano yan uwan juna ne su na jini a yayin da ya bayyana ta ga iyayensa.

Da yake bayar da lamarin mawuyacin halin da ya shiga, Njoroge ya bayyana cewa Wanjiku kanwarsa ce, diyar matar babansa ta biyu, kamar yadda ya shaida ma Kameme TV.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng