Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano

- A yau, Lahadi, ne al'ummar Musulmi a fadin Najeriya su ka yi Sallar Idi bayan kammala azumin watan Ramadana

- Ba a gudanar da Sallar Idi a Masallatai ba a jihohin Najeriya da dama saboda annobar cutar korona

- Jihar Kano na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da gwamnoni su ka amince a gudanar da Sallar Idi a cikin Jam'i a Masallatai

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnoni shida na yankin arewa da suka hada da Gwamna Ganduje na jihar Kano sun dage dokar hana jam'i a jihar don samu a yi sallar Idi.

Jama'a da yawa sun kalubalanci wannan matakin don ya saba wa shawarar kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona da kuma hukumar NCDC.

A ranar Juma'a, 23 ga watan Mayu, shugaba Buhari da kungiyar gwamnoni sun yi taro inda suka amince da bude wuraren bauta tare da yin sallar jam'i amma kada a zarta mutum 50.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya tabbatar da cewa yin taron ya hada har da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN).

DUBA WANNAN: Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Atiku Abubakar

Gwamna Umar Ganduje na jihar Kano ya shawarci malaman addinin islama a jihar da su gabatar da gajeriyar huduba yayin sallar idi wacce ya aminta da a yi duk da gwamnatin tarayya ta soki hakan.

A wata takarda da sakataren yada labaran gwamnan ya fitar a ranar Asabar, Abba Anwar ya ce za a yi sallar idi a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Ya ce dole ne Musulmi su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka tanadar don sallar jam'i.

"Kamar yadda manyan Malamai suka shawarci limamanmu, ya kamata a yi huduba gajera a yayin sallar Idin saboda kalubalen COVID-19 da muke fuskanta.

"Akwai bukatar jama'a su hanzarta watsewa ana kammala sallar sannan su ci gaba da kiyaye dokokin kiwon lafiya," kamar yadda takardar ta kunsa.

Sai dai, a wasu hotunan Sallar Idi daga Masallacin unguwar Bompai a cikin Kano da jaridar Daily Trust ta wallafa, jama'a sun gudanar da Sallah cikin jam'i ba tare da kiyaye dokar nesanta ba.

Kazalika, jaridar 'TheCable' ta wallafa hotunan Sallar Idi daga Masallacin idi na kofar, inda sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, su ka halarta.

TheCable ta bayyana cewa babu wata nesanta a tsakanin jama'a yayin da su ka halarci Masallacin domin yin Sallar Idi a cikin jam'i.

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Asali: Twitter

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Asali: Twitter

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Asali: Twitter

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Asali: UGC

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Asali: UGC

Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel