Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.

Wannan shi zaman majalisar na biyu da shugaban kasar yake jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna, wadda ta zama doka ta farko da aka fara bi tun a zaman majalisar na makon da ya gabata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, 'yan majalisar kalilan ne suka hallara a zauren da ake gudanar da taron, yayin da dama suke halartarsa ta hanyar bidiyo da aka hada da yanar gizo.

Zaman majalisar zartarwa
Hakkin mallaka: Femi Adesina
Zaman majalisar zartarwa Hakkin mallaka: Femi Adesina
Asali: Facebook

Zaman majalisar zartarwa
Hakkin mallaka: Femi Adesina
Zaman majalisar zartarwa Hakkin mallaka: Femi Adesina
Asali: Facebook

Zaman majalisar zartarwa
Hakkin mallaka: Femi Adesina
Zaman majalisar zartarwa Hakkin mallaka: Femi Adesina
Asali: Facebook

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Sama da mutane 500 aka kashe a jihohi 10 cikin watanni 3

Zaman majalisar zartarwa
Hakkin mallaka: Femi Adesina
Zaman majalisar zartarwa Hakkin mallaka: Femi Adesina
Asali: Facebook

An gudanar da makamacin wannan zama a ranar Laraba ta makon da ya gabata, yayin da shugaba Buhari ya tabbatar da nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.

Majalisar ta zabi sauya salon zaman majalisar ne ta hanyar ba da tazara domin kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta da manufar dakile yaduwar cutar korona da ta zamto ruwan daren da ya game duniya.

Ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a fadar shugaban kasa.

Wadanda suka halarci zaman majalisar sun hadar da mataimakin shugaban kasa; Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da babban mai ba da shawara a kan tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

Haka zalika sauran mahalartan sun hadar da Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, Ministar Kudi; Zainab Ahmed, Ministan Ilimi; Adamu Adamu, Ministan Shari'a; Abubakar Malami, Ministan Sufuri; Rotimi Amaechi, Ministan Ayyuka da Gidaje; Babatunde Fashola da kuma Karamin Ministan Man Fetur; Timipre Sylva.

Bayan bude taro da addu'a, Boss Mustapha ya nemi a yi shiru na tsawon minti daya domin karrama tsohon ministan Najeriya, Alhaji Muhammad Bello Dogondaji, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a, 15 ga watan Mayu.

Marigayi Bello Dogondaji ya rike mukamin karamin ministan ilimi a tsakanin shekarar 1993 zuwa 1994 a gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel