Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya bude wuraren bauta, za a yi sallar Idi

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya bude wuraren bauta, za a yi sallar Idi

- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bi sahun wasu daga cikin takwarorinsa

- Ya janye dokar da aka sanya a wuraren bauta a jihar

- Bala Mohammed ya kuma sanar da cewar za a yi sallar idi a fadin jiharsa

Gwamnan Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sanar da bude wuraren bauta a fadin jihar daga gobe Alhamis, 21 ga watan Mayun 2020.

Bala Mohammed ya kara da cewa za a yi sallar Idi a fadin jihar Bauchi baki daya, jaridar Blueprint ta ruwaito.

Wannan mataki na gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin takwarorinsa suka janye dokar kulle a jihohinsu.

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya bude wuraren bauta, za a yi sallar Idi
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Bauchi ya bude wuraren bauta, za a yi sallar Idi Hoto: Senator Bala A. Mohammed
Asali: Twitter

A wani labarin kuma, Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i, ya yi watsi da yiwuwar sassauta dokar kullen da ya shimfida a jihar a yunkurin dakile yaduwar cutar korona.

Malam El-Rufa'i a ranar Talata, 19 ga watan Mayu, ya ce ba zai yi gaggawar cire dokar kullen da ya shimfida ba a jihar a sanadiyar yadda ba a samu wani rangwami ba na yaduwar cutar korona.

KU KARANTA KUMA: Sallar Idi: Zulum ya umarci limamai da kwamitin yaki da COVID-19 su tattauna

Tun a ranar 26 ga watan Maris ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga, inda kuma a ranar 26 ga watan Afrilu, ta sake tsawaita dokar har na tsawon kwanaki 30.

Tsohon Ministan na Abuja ya hau kujerar naki tare kawar da kai a kan rokonsa da ake ci gaba da yi na neman a sassauta dokar kullen domin samun damar gudanar da Sallar Idi, wadda ake sa ran kasancewarta a ranar Asabar ko Lahadi.

A sanadiyar haka ma ya ce shi da kansa zai fita ya tsare iyakar Kano da Kaduna domin tabbatar da an kiyaye dokar hana zirga-zirga a ranar Sallah.

Gwamnan ya ce zai yi hakan ne domin ya tabbatar babu wani mutum da zai shigo Kaduna daga Kano.

Ya ce gwamnatinsa ta na ci gaba da shirin sassauta dokar kullen, sai dai fa babu rana domin kuwa ya danganta da yadda lamari na annobar korona zai kasance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel