'Ku taimaka ku sakeni, lafiyata kalau' - Bidiyon mai jinyar korona tana rokon NCDC
Susan Idoko Okpe, mace ta farko da aka sanar ta kamu da cutar korona a jihar Benuwe, ta sake rokon gwamnatin Najeriya a kan ta saketa daga cibiyar killacewa ta Abuja bayan ta shafe kwanaki 57.
A wani sabon faifan bidiyo da ta nada ranar Talata, Susan ba ta san me NCDC ke nufi da ita ba tare da yin zargin cewa ana son kasheta ko ba ta guba.
Susan ta kafe a kan cewa lafiyarta kalau kuma tunda aka kaita cibiyar killacewa ba a duba lafiyarta ba.
Ta bayyana cewa sau biyar ana yi mata gwajin kwayar cutar korona amma ba a sanar da ita sakamakon gwajin.
Ta roki hukuma da mahukunta a kan saketa, su kyaleta ta koma gida wurin iyalinta domin cigaba da rayuwa cikin 'yanci.
"An yi min gwaji na farko, na biyu, na uku da na hudu amma su na cewa na ki amincewa a sake yi min gwaji. An sake daukan jinina ranar Alhamis domin yi min gwaji na biyar.
"Ina son 'yan Najeriya su taimakeni, su tambayi NCDC me suke nufi da ni?
"Lafiyata kalau, ban taba yin rashin lafiya ba tunda aka kawoni nan tsawon kwanaki 57 da suka gabata.
"Ba su bani wani magani ba. Ban yi rashin lafiya ba, babu ciwon ko kai, ban yi tari ba, amma har yanzu ina nan a kulle, babu wanda ya ke zuwa ya wurina, na gaji," a cewar Susan.
A ranar Litinin ne daya daga cikin ma su jinyar korona da aka sallama daga cibiyar killacewa a jihar Delta ta yi zargin cewa damfara kawai ake yi da sunan cutar a Najeriya.
DUBA WANNAN: Bidiyon yadda ma su jinyar korona ke raha da wasan 'yar wulliya a cibiyar killacewa a Abuja
Matar, mai shekaru 36, ta kamu da cutar korona a ranar 17 ga watan Afrilu bayan an yi jayayya da ita a kan sakamakon gwajin kwayar cutar da aka yi mata.
Daga bisani an dauketa zuwa cibiyar killace ma su cutar korona da ke garin Warri, inda ta shafe kwanaki 17 ta na jinya kafin daga karshe a sallameta.
Yayin ganawarta da manema labarai bayan an sallameta, matar ta kafe a kan cewa damfara kawai ake yi da sunan cutar a Najeriya, saboda har yanzu ba ta ga sakamakonta da ya nuna cewa ta na dauke da kwayar cutar ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng