Fallasar Dan APC Ta Jawo Atiku Ya Sake Huro Wuta ga Tinubu
- Atiku Abubakar ya buƙaci Tinubu ya bayyana waɗanda suka karɓi biliyoyin naira da ake zargin wasu ministoci sun biya domin samun muƙamai a gwamnatinsa
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da tsananta tsadar rayuwa da kuma hana ma’aikatu kuɗaɗen gudanar da ayyukansu
- Alwan Hassan, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, ya yi zargin cewa wasu ministoci sun biya kuɗaɗe masu yawa domin samun muƙamai, amma bai bayyana sunayensu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ministocinsa.
Atiku ya kalubalanci Shugaba Tinubu da ya bayyana sunayen jami’an da ake zargin sun karɓi cin hanci daga wasu ministoci domin naɗa su muƙamai a gwamnatinsa.

Source: Twitter
Atiku ya yi wannan ƙalubale ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoban 2026.
A cikin sakon, Atiku ya nemi Tinubu ya bayyana waɗanda ake zargin sun karɓi biliyoyin Naira daga mutanen da ke neman muƙaman ministoci.
Wannan martani na Atiku ya biyo bayan zargin da Alwan Hassan, mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya yi cewa wasu ministoci sun biya biliyoyin naira domin samun muƙamai, sannan suka mayar da hankali wajen dawo da kuɗin bayan naɗinsu.
Wace bukata Atiku ya nema wajen Tinubu?
A saƙon da ya wallafa, Atiku ya ce ya kamata shugaban ƙasar ya bayyana waɗanda suka karɓi kuɗin da ake zargin an biya domin samun muƙamai a gwamnatinsa.
“Bola @officialABAT, kakakin yaƙin neman zaɓenka ya amince cewa ministoci sun biya biliyoyin naira a matsayin cin hanci domin samun naɗin muƙamai. Kai ne ka naɗa su, to wa ya karɓi kuɗin? ’Yan Najeriya sun cancanci sanin sunaye, ba shiru ba,” in ji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna cewa bai kamata a bar zargin ya tsaya ba tare da an bayyana waɗanda abin ya shafa ba.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata gwamnati ta ba ’yan Najeriya amsoshi kan zargin da ya shafi naɗe-naɗen jami’an gwamnati.
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan tsadar rayuwa
Baya ga zargin cin hancin, Atiku ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan tsadar rayuwa da kuma yadda take gudanar da kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatun gwamnati.
A cewarsa, wasu matakan da gwamnatin ta ɗauka sun taimaka wajen ƙara tsananta halin matsin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ya kuma nuna damuwa kan zargin cewa ana hana wasu ma’aikatu kuɗaɗen gudanar da ayyukansu saboda rashin amincewa da ministocin da ke jagorantarsu.
“Matakan da gwamnatinka ta ɗauka ba tare da yin la’akari da sakamakonsu ba sun jefa jama’a cikin matsalar tsadar rayuwa. Sannan idan ka hana ma’aikatu kuɗaɗe saboda ba ka yarda da ministocinka ba, ’yan Najeriya ne ke jin wahalar gwamnatin da ta yi watsi da su,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya fito ya yi maganar dalilin da ya sa Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba

Source: Twitter
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Bola Tinubu kan ware makudan kudi saboda tunkarar cutar Ebola.
Atiku ya bukaci Tinubu ya yi bayani kan Naira biliyan 10 da aka amince a ware domin shirin tunkarar cutar Ebola a watan Yunin shekarar 2026.
Asali: Legit.ng

