An Ƙara wa Abba Kabir Ƙarfin Tallar APC bayan Abin Alherin Tinubu a Kano
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sababbin tashoshin wutar lantarki guda huɗu a Kano, waɗanda za su ƙara ƙarfin rarraba wutar lantarki
- Ayyukan da TCN ta gudanar tare da gwamnatin Kano sun shafi Walalambe, Kumbotso, Dakata da Dan-Agundi domin inganta samar da wutar lantarki ga al'umma
- Kamfanin Lee ya koma amfani da wutar lantarkin ƙasa bayan shekaru sama da 30, yayin da gyaran tashar Dan-Agundi zai inganta wutar tsohon Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sababbin tashoshin wutar lantarki guda huɗu a Kano.
Ana hasashen tashoshin za su ƙara ƙarfin isar da wutar lantarki da megawatt 544, domin inganta samar da lantarki ga masana'antu, kasuwanci da gidaje.

Source: Facebook
Kano: An ƙaddamar da tashoshin wutar lantarki
Kamfanin rarraba wutar lantarki (TCN) ne ya gudanar da ayyukan tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kano, inda aka gina tashoshin a Walalambe, Kumbotso, Dakata da Dan-Agundi, cewar Punch.
Wata sanarwa da mai ba ministan lantarki shawara kan yaɗa labarai, Adeola Labzy, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, ta bayyana cewa sabbin kayan aikin za su rage cunkoso a tashoshin da ke ɗauke da nauyi fiye da ƙarfinsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa ayyukan za su inganta isar da wutar lantarki mai yawa, tare da samar da damar biyan buƙatun masu amfani da wutar lantarki waɗanda a baya ba a iya biya ba.
A tashar Walalambe, aikin ya samar da ƙarfin megawatt 80 ta hanyar amfani da tiransifoma guda biyu, kowannensu mai ƙarfin 40MVA, cewar Vanguard.
Tashar tana da layukan fitar da wutar lantarki guda shida waɗanda za su rarraba wuta zuwa yankin masana'antu na Tokarawa, Eastern Bypass, hanyar Maiduguri, hanyar Hadejia da sauran al'ummomin da ke makwabtaka.
Sanarwar ta ce:
“Ma'aikatar Lantarki ta Tarayya, ta hannun Kamfanin Transmission Company of Nigeria, tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kano, ta ƙaddamar da tashoshin wutar lantarki guda huɗu waɗanda suka ƙara ƙarfin isar da lantarki da megawatt 544 a Kano da babbar hanyar sadarwar lantarki ta ƙasa.
“Waɗannan tashoshi suna Walalambe, Kumbotso, Dakata da Dan-Agundi. Walalambe ta samu sabon ƙarfin megawatt 80, tare da tiransifoma guda biyu masu ƙarfin 40MVA kowannensu.
“Kumbotso ta samu kayan aikin lantarki masu ƙarfin 330kV da tiransifoma masu ƙarfin 100MVA. Dakata da Dan-Agundi kuma kowannensu ya samu ƙarin tiransifoma mai ƙarfin 100MVA a matakin 132kV.”

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira

Source: Original
Sanarwar ta bayyana cewa rukunin Lee, wani babban kamfanin masana'antu, ya koma amfani da wutar lantarki daga babbar hanyar sadarwar ƙasa bayan ya shafe sama da shekaru 30 yana amfani da wutar da yake samarwa da kansa.
Aikin da manyan tashoshin za su yi
A tashar Kumbotso, aikin ya ƙunshi kayan aikin lantarki masu ƙarfin 330kV da tiransifoma masu ƙarfin 100MVA.
Haka kuma, tashoshin Dakata da Dan-Agundi sun samu ƙarin tiransifoma mai ƙarfin 100MVA kowannensu a matakin 132kV, domin ƙara ingancin samar da lantarki.
Gyaran tashar Dan-Agundi na da muhimmanci musamman saboda gobarar da ta lalata ta a baya. Ma'aikatar ta ce gyaran ya dawo da wani babban ɓangare na ƙarfin tashar.
Abba Kabir ya taya Kwankwaso murna
Mun ba ku labarin cewa Abba Kabir Yusuf, ya fitar da jawabi domin taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 70 a ban kasa.
Mai girma gwamnan ya yaba da gudunmawar Kwankwaso wajen ci gaban jihar Kano, siyasa da dimokuraɗiyya.
Ya roƙi Allah SWT Ya ƙara wa tsohon gwamna lafiya, tsawon rai da ƙarfin ci gaba da yi wa al'umma hidima.
Asali: Legit.ng


