Ni da kai na zan fita tsare iyakokin Kaduna-Kano a ranan Sallah — El-Rufai

Ni da kai na zan fita tsare iyakokin Kaduna-Kano a ranan Sallah — El-Rufai

- Gwamnan Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya ce shi da kansa zai fita domin tsare iyakokin Kaduna da Kano a ranar Sallah

- Gwamnan ya ce ya zai yi hakan ne domin ya tabbatar babu wani mutum da zai shigo Kaduna daga Kano

- El Rufai ya koka kan yadda wasu jamian tsaro ke karbar kudi a hannun direbobi suna barinsu su shigo Kaduna duk da dokar hana zirga zirga tsakanin jihohi da gwamnati ta saka

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shi da kansa zai fita domin tsare iyakokin Kaduna da jihar Kano a ranar Sallah domin tabbatar da cewa babu wani da ya shigo jiharsa daga Kano a yunkurinsa na dakile yaduwar cutar.

Ana sa ran za a gudanar da bikin sallar na wannan shekarar a ranar Asabar ko Lahadi ne idan azumin watan Ramadan ya zo karshe.

Ni da kai na zan fita tsare iyakokin Kaduna-Kano a ranan Sallah — El-Rufai
Ni da kai na zan fita tsare iyakokin Kaduna-Kano a ranan Sallah — El-Rufai. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita inda ta ware wa mutane kwanaki biyu domin su fita su siya kayayyakin da suke bukatar a ranakun Laraba da Alhamis don tabbatar da kowa ya zauna a gida a karshen makon.

DUBA WANNAN: Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD

El Rufai ya yi wannan gargadin ne a yayin hira da aka yi da shi a wasu gidajen rediyo a ranar Talata inda ya ce; "Da kai na zan fita in rika zaga iyakokin Kaduna da Kano kuma ba zan bar wurin ba sai dare don in ga wanda zai shigo Kaduna. Ba zan bar wurin ba sai dare."

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda mutane ke shiga da fita jihar duk da umurnin shugaban kasa na hana zirga zirga tsakanin jihohi, inda ya ce galibin wadanda suke dauke da cutar a jihar sunyi tafiya.

Ya jingina laifi a kan wasu jamian tsaro marasa kishin kasa da ke karbar cin hanci a hannun matafiya su barsu su shigo jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El Rufai ya ce, "Ba abinda ba mu yi ba amma jamian tsaro ba su bamu hadin kai. Mun samu labarin yadda wasu direbobin motocin haya da wasu ke biyansu kudi don su shigo Kaduna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel