Babban Alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma, ya rasu

Babban Alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma, ya rasu

- Allah ya yi wa babban alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma rasuwa

- Kamar yadda majiya daga iyalansa ta bayyana, marigayin ya rasu ne a daren ranar Litinin, 18 ga watan Mayu

- Ya kwashe tsawon shekaru tara yana rike da mukamin babban alkalin jihar, tun zamanin tsohon gwamna Ibrahim Geidam

Babban alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a daren ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, bayan yar gajeriyar rashin lafiya a asibitin kasa da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan.

Wani daga cikin iyalan marigayin, Hussaini Nabaruma, ne ya tabbatar da hakan ga Channels Television a ranar Talata, 19 ga watan Mayu.

Babban Alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma, ya rasu
Babban Alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma, ya rasu Hoto: Channels Television
Asali: UGC

Ya yi aiki a matsayin babban alkalin Yobe na kimanin shekaru tara, mafi tsayi a tarihin jihar.

Tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Geidam ne ya nada Justis Nabaruma a shekara ta 2011.

A wani labarin kuma, Sanannen malami kuma shugaban majalisar limaman jihar Kano, Falalu Dan Almajiri, ya rasu. Marigayin limamin ya rasu ne a sa'o'in farko na yau Talata, 19 ga watan Mayun 2020.

Wata majiya daga iyalansa ta ce ana shirye-shiryen birne marigayin a halin yanzu, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada Kashim Ibrahim-Imam shugaban TETFUND

A watan Nuwamban 2018, Dan Almajiri ya yi murabus a matsayin shugaban majalisar zartarwa ta hukumar walwalar alhazan jihar Kano, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Tun daga bullar annobar korona a kasar nan, ana ci gaba da fuskantar mace-mace a jihar Kano ballantana a tsakanin dattawa.

Duk da har yanzu a hukumance babu wata alaka da ta danganta mace-macen da annobar, akwai zargi mai matukar karfi da ke dangana hakan da cutar COVID-19 a jihar.

Mun kuma ji cewa a kalla mutum 197 ne wadanda ake zargi da laifuka daban-daban da ya hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar motoci da kwacen adaidaita ne suka shiga hannun 'yan sandan jihar Kano.

An kama wadanda ake zargin tsakanin ranar 11 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Mayu a yankuna daban-daban na jihar. Rundunar Operation Puff-Adder ne suka yi wannan kamen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel