Kashe-kashen Kaduna: El-Rufai ya kira taron shugabannin tsaro da masu ruwa da tsaki

Kashe-kashen Kaduna: El-Rufai ya kira taron shugabannin tsaro da masu ruwa da tsaki

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai a ranar Juma'a ya yi taro da shugabannin cibiyoyin tsaro na jihar tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya kira taron ne don tattaunawa tare da shawo kan matsalar kashe-kashen da ke aukuwa a jihar ballantana na Kajuru da ya faru a makon da ya gabata.

A yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron a gidan gwamnatin jihar, Yakubu Umar Barde, dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun/Kajuru a tarayya ya yi kira ga jama'ar yankin da su zauna lafiya.

Barde, wanda dan jam'iyyar adawa ta PDP ne, ya ce gwamnan zai dauka dukkan matakan tsaron da za su kawo zaman lafiya a yankin.

Kamar yadda yace, "Mun tattauna halin tsaro da yankin Kajuru ke ciki ne tare da Malam Nasir El-Rufai tare da masu ruwa da tsaki.

Kashe-kashen Kaduna: El-Rufai ya kira taron shugabannin tsaro da masu ruwa da tsaki
Kashe-kashen Kaduna: El-Rufai ya kira taron shugabannin tsaro da masu ruwa da tsaki. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA: Turmi da tabarya: Matar aure ta mutu yayin da Fasto ke lalata da ita a gidansa

"Akwai bukatar kabilu su yarda da juna. Idan babu zaman lafiya, ba za a samu yarda da juna ba. Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su yi wa jama'ar su magana don samun zaman lafiya.

"Gwamnan na daukar dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro ingantacce. Gwamnan na bada goyon baya ga dukkan cibiyoyin tsaro don su dawo da zaman lafiya a yankin."

Hakazalika, kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Umaru Muri, ya ce an kara tura jami'an tsaro a yankin kuma an saisaita al'amuran.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da ja kunnen yankunan da abun ya shafa.

"Mun tattauna a kan hare-haren da ake kaiwa yankin Kajuru. Ba za mu sassauta ba. Muna matukar kokarin mu wajen kawo zaman lafiya mai dorewa a Kajuru.

"Mun tura jami'an tsaro yankin kuma a halin yanzu komai ya daidaita," yace.

A bangaren hakimin Kufana, Titus Dauda, wanda ya halarci taron, ya ce "Muna bukatar zaman lafiya a Kajuru. Muna da kabilun Adara, Fulani, Hausa da sauransu. Muna da tabbacin zaman lafiya zai dawo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel