Zamfara: Shugaban 'yan bindiga ya fitar da sautin murya, ya ja kunnen jama'a da kakkausar murya

Zamfara: Shugaban 'yan bindiga ya fitar da sautin murya, ya ja kunnen jama'a da kakkausar murya

A wani sautin murya da jaridar HumAngle ta samu, shugaban 'yan bindiga, Kachallah, ya ja kunnen mazauna Shinkafi da kada su kuskura su bar sojojin Najeriya a tsakaninsu.

Ya fitar da wannan sakon ne bayan tsanantar ayyukan dakarun sojin Najeriya a yankin don tarwatsa 'yan ta'addan.

"Ta yaya sojoji za su dinga kashe min jama'a bayan tattaunawa muke. A kan mene za su fito neman 'yan bindiga?

"Na rantse da Ubangiji idan har suka kara kawo mana hari sai mun kashe 40 a nan, 50 a can, 30 a can kuma duk a rana daya. Na san za su so harar mu amma makoki ba zai bar su ba.

"Na rantse da Ubangiji, matukar kuka bar dakarun soji suka tsallako Shinkafi, ba za ku iya ciyar da 'yan gudun hijira ba," ya ja kunne.

"Na basu kwana uku, idan basu daina ba, za mu zaba wasu yankuna. Sai mun kashe mutum 100 a Kurya. Za mu kori mutane daga yankuna masu tarin yawa.

"Abinda suke so shine mu ajiye makamai sannan mu tafi babu komai. Ai hakan ba za ta yiwu ba. Gara mu mutu kawai.

"Sun kwace mana sama da makamai 30, sun kwace mana babura sama da 60. Haka ake neman zaman lafiya?

"Muna jiran zuwan su. Ban je ko ina ba, ina jiran sojojin," Kachallah yace.

Ya kara da jaddada cewa ba za su sassauta wa kowacce karamar hukuma ba matukar ta bar sojoji suna taimakon ta.

"Wadannan mutanen za su kammala aikin su koma Abuja. Gwamnati za ta ci gaba da biyan su kuma za su bar mu tare. Kada ku bar su su wuce ta Shinkafi, sun san ta inda ya kamata su bi.

Katsina: Shugaban 'yan bindiga ya fitar da sautin murya, ya ja kunnen jama'a da kakkausar murya
Katsina: Shugaban 'yan bindiga ya fitar da sautin murya, ya ja kunnen jama'a da kakkausar murya. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Oyo

“Ku sani, ina yaki da Zurmi, matukar kuka bar su suka wuce ta Shinkafi, na rantse babu wani kauye da za mu bari su kara bacci. Za mu cika ku da 'yan gudun hijara kuma za ku yi ta birne mutanen ku.

"Ba za mu ci gaba da zuba ido muna gani ana mana rashin adalci ba, an kashe mana mutane.

"Na rantse da Ubangiji na bai wa mutane na umarnin kashe kowa. Za mu tabbatar da an daina noma.

"Za mu ga yadda za ku rayu da cutar korona da kuma yunwa," Kachallah yace yayin da yake umarni ga yaran shi da su kasance cikin shiri.

Kachallah na wannan gargadin ne sakamakon kashe 'yan bindigar da aka yi a yankin Zurmi.

Rundunar sojin sun yi nasarar kwace makaman su masu tarin yawa da baburan su.

Shugaban 'yan ta'addan ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna halin ko-in-kula ga kabilar Fulani.

"Najeriya bata da makiyi kamar Muhammadu Buhari, tunda ya hau mulki bai taba tallafa wa bafulatani ko daya ba," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel