Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa

Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa

Mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Tafoki ya samu damar yi wa zauren majalisa jawabi amma sai ya fashe da kuka a kan rashin tsaron da ya addabi mazabar Faskari.

Yankunan sun saba samun hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro.

A makon da ya gabata, mutum biyar suka halaka sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majalisar jihar, ya ce ba a samun rana daya a halin yanzu da za ta wuce ba tare da an ji harin da aka kai yankin ba.

Kamar yadda yace, karamar hukumar Faskari a halin yanzu za a iya kwatanta ta da Maiduguri, "Ko a daren jiya 'yan bindiga sun kai hari garin Daudawa inda suka yi garkuwa da mutum 4 sannan suka raunata wasu."

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Tafoki na wannan jawabin ne yayin da ya fashe da kuka a zauren majalisar, lamarin da yasa ya kasa ci gaba da jawabin don haka ya koma mazauninsa.

Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa
Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Atiku da Saraki sun yi martani a kan nadin Farfesa Gambari

Bayan shi, a kalla 'yan majalisar bakwai ne suka yi jaje da korafin abinda ke faruwa a mazabarsu.

AbdulJalal Runka, dan majalisa mai wakiltar mazabar Safana ya roki gwamnatin jihar da ta sassauta dokar hana walwala a yankinsa don kullum sai an kai musu hari tare da kwashe musu dabbobin su.

Ya ce sassauta dokar za ta basu damar siyar da sauran dabbobin na su don samun abinda za su ci a maimakon 'yan bindigar su yi ta sacewa.

Ibrahim Machika, dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabuwa ya ce matukar gwamnati ba za ta iya shawo kan wannan matsalar tsaron ba, toh a saukesu ko kuma a bar jama'a su kare kansu.

Hakazalika, Jabiru Yau dan majalisa mai wakiltar mazabar Batsari ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kula da halin da Katsinawa ke ciki.

A kalla kananan hukumomi 14 na jihar Katsina ne a koda yaushe suke fuskantar hare-haren 'yan bindigar wanda ke kawo rasa rayuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel