Shekau ya saki sabon sako ranar Laraba, ya yi karin bayani a kan faifan sautin da ya yi kuka

Shekau ya saki sabon sako ranar Laraba, ya yi karin bayani a kan faifan sautin da ya yi kuka

A yayin da rahotanni a ranar Talata suka wallafa labarin cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fashe da kuka yayin da yake neman tsari daga dakarun sojin Najeriya, sai ga shi ya musanta hakan a ranar Laraba.

A cikin wani takaitaccen sako da fitaccen lauyan nan mazaunin jihar Kano, Bulama Bukarti, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya ce Shekau ya karyata batun cewa ya fara saduda, inda ya ce tsohon bidiyo ake yadawa.

A cewar Bukarti, Shekau ya sake yi masa barazana tare da yin gargadi na musamman ga wani dan jarida, Ahmad Salkida, a kan cewa ya bi a hankali.

Kazalika, ya ce Shekau ya jaddada zamansa daram a kan akidunsa tare da yin shagube ga kungiyar G5 ta kasashen yankin sahel.

"Shekau ya saki sabon sakon sautin murya tare da karyata bidiyonsa da aka yada jiya (Talata). Ya sabunta barazanarsa a kaina, sannan a karon farko ya gargadi Ahmad Salkida ya bi a hankali. Ya yi izgili ga kungiyar G5 ta kasashen Sahel, sannan ya bayyana cewa yana nan daram a kan akidunsa kamar aka sansu," a cewar Bukarti

Saurarai faifan sautin muryar Shekau na farko a nan:

Saurarai faifan sautin muryar Shekau na biyu a nan:

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa cewa a cikin wani sabon sako na daukan sauti, an ji muryar jagoran kungiyar ta'adda ta Boko Haram, Abubakar Shekau, yana rusa kuka yana neman kariyar Allah daga sojojin Najeriya.

A 'yan kwanakin baya bayan nan, rundunar sojojin Najeriya ta kara kaimi wajen kai hare-hare, tare da samun jerin nasarori a kan 'yan Boko Haram musamman a yankunan da ke gabar tafkin Chadi.

DUBA WANNAN: Za a cigaba da sallar Juma'a a Masallatan jihar Jigawa

Cikin sakon daukan sauti na tsawon minti daya da dakiku 22 da jaridar Daily Nigerian ta saurara, an ji muryar Shekau cikin harshen Kanuri yana neman kariyar Allah daga wutar da sojojin Najeriya suka kunno masa.

Shekau ya misalta matsin lambar da sojojin Najeriya suka yi masa a matsayin 'aikin shaidan', lamarin da ya ce shi da mabiyansa suna cikin mawuyacin hali a wannan wata mai Albarka na Ramadana.

"In dai zaluncin sojojin Najeriya ne, to Ya Allah ka tsare mu daga sharrrinsu. Ya Allah ka tabbatar da mu a kan addininka. Ya Allah babu abin da muka sani kuma babu abin da zamu iya isarwa kawunanmu. Kai ne mai jibintar lamarin Ya Ubanginjinmu."

"Mun kaurace wa Izala saboda mu yi addininka na gaskiya; mun bar Tijjaniya saboda mu daidaita a kan tafarkin ka na gaskiya; mun barranta daga Shi'a domin yin addininka na gaskiya; mun bar iyayenmu da 'yan uwanmu domin mu tsira da addininka na gaskiya."

"Saboda addininka muke yanka wuyan bayinka da wuka; amma a yau suna kokarin sauya mu zuwa wani addini sabanin naka. Ya Ubangiji kayi mana rahama domin falalar watan Ramadan; Ya Allah ka kawo mana sauki a cikin wannan wata mai Albarka.

"Ya Allah ka bamu nasara a kan makiyanmu. Ya ku yan'uwa don Allah, ku yiwa Allah biyayya ku taimaka min da addu'o'i ta neman kariyarsa.

"Ya Allah ka mu ikon riko da Alkur'ani. Allah kai ne mafi sani. Tsira da aminci su tabbata a kan Annabin ka, kuma dukkanin godiya ta tabbata a gare ka," Shekau ya fada cikin shessheka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel