Mai shari’a Isiaka Isola Oluwa ya kwanta dama a shekara 102

Mai shari’a Isiaka Isola Oluwa ya kwanta dama a shekara 102

- Alkali Isiaka Isola Oluwa ya rasu ya na da shekaru fiye da 100

- Isiaka Oluwa ya yi karatun ilmin shari’a a Landan tun a 1950s

- Cif Bode George da Musliu Obanikoro sun ce Legas ta yi rashi

A ranar Asabar ne Ubangiji ya yi wa tsohon alkali Isiaka Isola Oluwa wanda ke Legas rasuwa. Marigayin ya cika ne a cikin gidansa, kuma tuni aka bizne shi tun a ranar.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an bizne Isiaka Isola Oluwa a makarbartar musulmai ta Atan da ke garin Yaba. Alkalin ya rasu a ranar da aka tashi da azumi na 15.

Isola Oluwa mai rasuwa shi ne tsohon alkalin da ya fi kowane tsufa a jihar Legas. Tarihi ya nuna cewa an haife sa ne ranar 23 ga watan Yuni, 1918 a yankin jihar Kuros-Riba.

Iyayen marigayin mutanen Legas ne da su ka tare a kudu maso kudancin kasar. Isola Oluwa ya halarci makarantar gwamnati ta Forcados da ta St Bartholomew da ke Sapele.

KU KARANTA: Wani babban Hadimin Gwamnan Jihar Jigawa Badaru ya rasu

Bayan haka marigayin ya halarci fitacciyyar makarantar nan ta King’s College ta Legas, sannan ya yi karatun gaba da sakandare a makarantar koyon aikin gona da ke Samaru.

Mai shari’a Isiaka Oluwa ya yi karatun ilmin shari’a a jami’ar Landan inda aka kira shi kuliya a 1957. Jaridar ta ce marigayi Oluwa ya taba yin aiki a matsayin malamin jami’a.

Mai rasuwan ya koyar a jami’ar Ibadan tsakanin 1949 zuwa 1950. Bayan haka marigayin ya yi aikin koyarwa da na malamin noma a makarantar aikin gona da ke garin Zariya.

A shekarar 1974 aka nada Isiaka Isola Oluwa a matsayin alkalin babban kotu. Bayan shekaru kusan goma ya na aiki a kotun tarayya Oluwa ya yi ritaya daga aiki a Yunin 1983.

Daga cikin wadanda su ka aikawa iyalin marigayin da mutanen Legas ta’aziyya akwai tsohon minista sanata Musiliu Obanikoro da jigon jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel