Ana siyasantar da batun annobar COVID-19, Almajirai inji Gwamna Ganduje

Ana siyasantar da batun annobar COVID-19, Almajirai inji Gwamna Ganduje

- Jihar Kano ta ce makwabtanta sun sa siyasa cikin harkar annobar Coronavirus

- Ganduje ya ce Kano ba ta surutu a kan wadanda su ka shigo mata da COVID-19

- Gwamna Ganduje ya zargi jami’an tsaro da sakaci wajen watsi da doka da ake yi

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi wasu gwamnonin jihohin Arewa game da hadarin siyasantar da sha’anin annobar cutar COVID-19 da kuma halin da almajirai su ke ciki a yankin kasar.

Mai girma Abdullahi Umar Ganduje, wajen wata zantawa da ‘yan jarida game da inda aka kwana wajen yaki da COVID-19 a jihar Kano, ya zargi wasu abokan aikinsa da rashin gaskiya.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jefi takwarorinsa da cusa siyasa a wajen yunkurin maida almajirai zuwa asalin jihohinsu da wasu gwamnatoci su ke yi a daidai wannan lokaci na annoba.

Idan ba ku manta ba, daga cikin daruruwan almajiran da gwamnatin jihar Kano ta maida jihohin da su ka fito kwanan nan, an samu wasu da-dama da ke dauke da kwayar cutar COVID-19.

KU KARANTA: Ma’aikatan lafiya 47 sun kamu da COVID-19 a Kano inji Kwamiti

Da ya ke hira da ‘yan jarida a Kano a ranar Lahadi, Abdullahi Umar Ganduje ya ce: “Abin da wadannan almajirai su ke bukata shi ne kulawa ba ayi ta ya-ma-di-di da labarinsu ba.”

Gwamna Ganduje ya karfafa cewa jihar Kano ta samu adadi mai tsoka na wadanda su ka shigo mata da cutar COVID-19, amma ta zabi ta killace su, ba tare da ta fito ta na wani surutu ba.

Bayan wannan gargadi da gwamnan na Kano ya yi wa makwabtansa, ya koka game da yadda mutanen jiharsa ke watsi da dokar da shugaban kasa ya sa, ya ce akwai laifin jami’an tsaro.

Bayan haka kuma gwamnatin Ganduje ta ja-kunnen malaman addinin musulunci da su ke shirin gudanar da sallar Juma’a da cewa su hakura da yin hakan domin zaman lafiyan kansu.

Bayan wannan rahoto da jaridar The Guardian ta fitar, idan za ku tuna gwamna Nasir El-Rufai ya fito ya na cewa an samu cutar COVID-19 a jikin almajirai 65 da aka dawo da su daga Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel