An sallami masu jinyar korona 6 bayan sun warke garau a Maiduguri

An sallami masu jinyar korona 6 bayan sun warke garau a Maiduguri

Labari da duminsa da Legit.ng ta samu daga kafar yada labarai ta TVC na nuni da cewa an sallami masu jinyar cutar korona 6 daga asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UMTH).

An sallami masu jinyar ne bayan an tabbatar da cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar, kamar yadda sakamakon gwajinsu ya nuna.

Hakan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen sako da TVC ta wallafa a shafinta na tuwita a ranar Lahadi.

Hudu daga cikin mutanen 6 da aka sallama, akwai ma'aikatan lafiya 4 da suka kamu da kwayar cutar yayin da suke aikinsu a sashen killace masu cutar a asibitin UMTH.

Sallamar mutanen na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da mutuwar karin wasu mutane biyu da ke jinyar cutar korona, lamarin da ya mayar da adadin mutanen da suka mutu saboda annobar a jihar zuwa mutane uku.

DUBA WANNAN: Gobara a asibitin masu jinyar cutar korona ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya ce sabbin mutanen biyu da suka mutu sune; wani babban mutum daga karamar hukumar Makarfi da kuma wata mata daga karamar hukumar Zaria.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, gwamnan ya ce an sake samun karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar, lamarin da ya mayar da adadin masu korona a jihar zuwa mutane 87.

A cewar gwamnan, mutane biyun da suka kamu da kwayar cutar sun hada da wani namiji daga karamar hukumar Igabi da wata mace daga karamar hukumar Chikun.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:20 na daren ranar Asabar, 09 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4151 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 745 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 128.

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 239 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:20 na daren ranar Asabar, 09 ga watan Mayu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel