Manyan mutane uku da suka mutu cikin sa'a 24 a jihar Yobe

Manyan mutane uku da suka mutu cikin sa'a 24 a jihar Yobe

- Annobar yawaitar mace - mace na cigaba da kara karfi a jihohin arewacin Najeriya

- Yawaitar mace - macen ta fi shafar tsofin mutane da ke fama da wasu cututtuka da su ka hada da hawan jini, ciwon sukari, ciwon koda da sauransu

- Mace - macen jama'a, wacce ke kama da irinta jihar Kano, ta fara jefa tsoro da zaman zulumi a tsakanin mazauna jihar Yobe

Wasu manyan mutane uku da suka yi suna sun mutu a cikin sa'a 24 daga cutar da ake zargin cewa annobar korona ce jihar Yobe, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

Manyan mutane sune; tsohon mamba mai wakiltar Nguru/Machina/Karasuwa/Yusufari a majlisar wakilai ta kasa, Alhaji Baba Bukar Machina, Muazu Buraji, darektan ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe, da Alhaji Bana Kura, wani sanannen ma'aikacin gwamnati a Geidam.

Machina ya mutu ne a cibiyar killacewa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kuma za a binne shi ranar Alhamis.

Da SaharaReporters ta tuntubi Mamman Mohammed, darektan yada labarai da kafafen sadarwa a Yobe, ya ce bashi da masaniya a kan abinda ya ke faruwa,

Ya bayyana cewa kwamishinan lafiya na Yobe zai gabatar da jawabi ga manema labarai a kan halin da ake ciki a jihar.

A ranar Laraba ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa a kalla mutum 155 ne su ka mutu a cikin kwanaki 6 a kananan hukumomin Gashua da Potiskum da ke jihar Yobe.

Manyan mutane uku da suka mutu cikin sa'a 24 a jihar Yobe
Manyan mutane uku da suka mutu cikin sa'a 24 a jihar Yobe Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

A cewar jaridar SaharaReportes, mutanen na nuna alamu da ke kama da na ma su dauke da kwayar cutar covid-19 kafin su mutu.

Yawaitar mace - macen, wacce ke kama da irinta jihar Kano, ta jefa tsoro da zaman zulumi a tsakanin mazauna kananan hukumomin.

DUBA WANNAN: Kaso 80 na ma su cutar korona ba sa bukatar a kwantar da su a asibiti - Shugaban PTF

Wani kwamitin bincike da shugaban kasa ya tura Kano ya alakanta yawaitar mutuwar mutanen jihar da annobar covid-19.

Wata majiya ta sanar da SaharaReporters cewa a kalla mutane 98 ne su ka mutu a karamar hukumar Potiskum a tsakanin ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, zuwa ranar Talata, 5 a watan Mayu.

"Babu wurin da ya kai makabartu cikar jama'a a garuruwan biyu a 'yan kwanakin nan.

"A kalla mutane 57, yawancinsu dattijai, sun mutu a garin Gashua. Amma duk da haka kwamitin kar ta kwana a kan covid-19 bai farka daga baccin da ya ke yi ba a Damaturu," a cewar wata majiyar SaharaReporters.

SaharaReporters ta yi zargin cewa gwamnan jihar Yobe ya tare a Abuja tun bayan zabensa, kuma har yanzu bai koma jiharsa ba domin fuskantar kalubalen da ya sako jama'a a gaba ba.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya bawa sarakunan jihar 14 kyautar motocin alfarma da kudinsu ya kai miliyan N600 duk da talaucin da jama'ar jihar ke fama da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel