Kaso 80 na ma su cutar korona babu bukatar a kwantar da su a asibiti - Shugaban PTF
Kwamitin shugaban kasa na kar ta kwana a kan annobar covid-19 (PTF) ya yi gargadi a kan ajiye ma su dauke da kwayar cutar korona da su ke da koshin lafiya a cibiyar killacewa.
Shugaban PTF, Dakta Sani Aliyu, ya shawarci gwamnatocin jihohi a kan kwantar da duk wani mai dauke da kwayar cutar korona, inda ya bayyana cewa zai fi dacewa a jiye kaso 80 na ma su dauke da cutar a wurare ma su kyau kamar Otal.
Dakta Aliyu ya bayar da wannan shawara ne ranar Laraba yayin taron da kwamitin PTF ya saba gudanarwa da manema labarai a kowacce rana.
Kazalika, ya shawarci jihohi su fara shiri na musamman a cibiyoyinsu na killacewa tare da samar da gadajen kwanciya da yawansu kar ya gaza 300.
Ya bayyana cewa ma su dauke da kwayar cutar da ba su galabaita ko nuna wasu alamun tsananin rashin lafiya ba, ba sa bukatar dawainiya mai yawa, kawai sa mu su ido za a yi da saka mu su wasu ka'idoji.
A cewarsa, ajiyesu a wurare kamar Otal zai bayar da damar samun isashen wuri a cibiyar killacewa da ya kamata a kwantar da wadanda kwayar cutar ke galabaitarwa, sannan zai saukakawa gwamnati kashe kudi.
Dakta Nasir ya roki dukkan 'yan kasa su dauki annobar korona da muhimanci tare da yin gargadin, "ya zama dole mu yi duk wani abu da zai dakile yaduwar cutar yayin da ake kan matakin dokar kulle."
DUBA WANNAN: An harbi DPO, an kashe mutane 5, an sace shugaban karamar hukuma a Katsina
A ranar Talata ne wasu masu dauke da cutar korona da ke jinya a cibiyar killacewa ta Kwadon da ke karamar hukumar Yamaltu Dena ta jihar Gombe sun fito zanga-zanga.
An gano cewa majinyatan na zanga-zangar ne sakamakon halin-ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna musu. Sun rasa abinci da magunguna duk da kuwa da killacesu da aka yi.
Wani mazaunin yankin wanda ya samu zantawa da jaridar SaharaReporters, ya ce, "tabbas sun baro cibiyar killacewar kuma a halin yanzu suna tarwatsa dukiyoyin jama'a a kan babban titin.
"Abin takaici ne yadda majinyatan suka fito zanga-zanga. Gaskiya gwamnati bata yi musu adalci ba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng