Zanga-zangar rashin abinci: Mun shawo kan matsalar majinyatan -Gwamnati

Zanga-zangar rashin abinci: Mun shawo kan matsalar majinyatan -Gwamnati

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta shawo kan matsalar rashin ciyarwa da majinyatan COVID-19 ke fuskanta a cibiyar killacewa ta jihar.

Wani mutum mai suna Buhari Tafida, wanda ya yi ikirarin shi majinyaci ne a asibitin koyarwa na jami'ar Abubukar Tafawa Balewa ya wallafa cewa ba a basu abinci har sai karfe 8 na dare a shafinsa na Twitter.

A wata takarda da Lawal Mu'azu, mai bada shawara na musamman ga gwamnan a kan yada labarai ya fitar, ya ce wannan jinkirin da suka yi na kaiwa majinyatan abinci ba da gangan bane.

"Hankalin gwamnatin jihar Bauchi ya kai ga koken da majinyatan COVID-19 ke yi na cewa ba a kai musu abinci da wuri. Tuni gwamnatin ta dauka matakin shawo kan matsalar a take," yace.

"Jinkirin kai musu abincin da aka yi ba da gangan bane kuma an yi dana-sani. Daya daga cikin majinyatan ya tabbatar da cewa an shawo kan matsalar kuma sun samun kular da ta dace.

"Gwamnatin jihar Bauchi ta dauka alkawarin duba duk wani kalubale da zai sa ta inganta jin dadin jama'ar jihar ballantana masu fama da muguwar cutar.

"Duk da karuwar yawan masu cutar da ake samu a jihar, gwamnatin jihar za ta yi kokarin ganin ta shawo kan yaduwar cutar a jihar," ya kara da cewa.

Zanga-zangar rashin abinci: Mun shawo kan matsalar majinyatan -Gwamnati
Zanga-zangar rashin abinci: Mun shawo kan matsalar majinyatan -Gwamnati. Hoto daga SaharaReporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Allah ya yi wa Kilishin Katsina, Alhaji Iro Sabe rasuwa

A jiya ne wasu majinyatan cutar coronavirus a jihar suka fito tare da yin zanga-zanga inda suka lalata wasu kayayyakin asibiti a jihar Gombe.

Majinyatan wandanda aka killace sun ce ana ba a kula dasu yadda ya dace da abinci ko magani.

Wasu masu dauke da cutar korona da ke jinya a cibiyar killacewa ta Kwadon da ke karamar hukumar Yamaltu Dena ta jihar Gombe sun fito zanga-zanga.

A ranar Talata ne majinyatan suka fito zanga-zangar tare da rufe babbar hanyar Gombe zuwa Biu.

An gano cewa majinyatan na zanga-zangar ne sakamakon halin-ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna musu. Sun rasa abinci da magunguna duk da kuwa killacesu da aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel