32 a Kano, 14 a Zamfara, 9 a Katsina a yayin da aka samu karin mutane 148 da annobar ta taba

32 a Kano, 14 a Zamfara, 9 a Katsina a yayin da aka samu karin mutane 148 da annobar ta taba

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 148 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:45 na daren ranar Talata, 05 ga watan Mayu, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 148 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

43-Lagos

32-Kano

14-Zamfara

10-FCT

9-Katsina

7-Taraba

6-Borno

6-Ogun

5-Oyo

3-Edo

3-Kaduna

3-Bauchi

2-Adamawa

2-Gombe

1-Plateau

1-Sokoto

1-Kebbi

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:45 na daren ranar Talata, 05 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 2950 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 481 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 98.

Duk da alkaluman NCDC na ranar Talata sun nuna an kara samun raguwar adadin mutanen da cutar ta harba, har yanzu rahotanni na cigaba da kawo labaran mutuwar mutane, musamman a jihohin arewa.

DUBA WANNAN: 'Rashin gaskiya ne': An bayyana dalilin da ya sa likitoci 10 su ka kamu da cutar covid-19 a AKTH Kano

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta sanar da mutuwar Saidu Ahmed, shugabanta na yankin arewa maso gabas.

Abdulkadir Ibrahim, shugaban sashen yada labarai na NEMA a yankin arewa maso gabas, ne sanar da mutuwar Ahmed yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ibrahim ya ce shugaban ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UMTH), inda aka kwantar da shi saboda ciwon sukari.

Kazalika, dan majalisar Borno mai wakiltar mazabar Bayo a majalisar jihar, Umar Audi ya rasu.

Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Maiduguri a yammacin ranar Talata kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

An ce ma'aikatan lafiya a asibitin sun dage cewa babu gadon da za a bashi inda suka ce gadon kawai da ya rage na mata masu haihuwa ne.

Amma iyalansa da suka kai shi asibitin sun yi nasarar shawo kan ma'aikatan asibitin, inda daga bisani suka karbe shi.

Majiyar ta ce, "ya mutu jim kadan bayan an bashi gado. An dauki samfuri daga jikinsa an aike wa Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, domin a tabbatar idan mutuwarsa na da alaka da COVID-19.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel