Tsohon gwamna Ali Modu ya yi wa ma'aikatan lafiya wayo, ya sulale ya gudu don kar a gwada shi

Tsohon gwamna Ali Modu ya yi wa ma'aikatan lafiya wayo, ya sulale ya gudu don kar a gwada shi

- Jama'ar Maiduguri sun nuna damuwarsu a kan rashin sanin inda tsohon gwamnansu, Ali Modu Sheriff, ya ke

- Tsohon gwamnan ya shiga wasan buya da jami'an cibiyar NCDC wadanda ke son su dauki jininsa domin a gwada shi

- Wata majiya mai kusanci da tsohon gwamnan ta sanar da SaharaReporters cewa tsohon gwamnan ya sulale zuwa Abuja tare da wasu tsirararn hadimansa

Mazauna Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun bayyana damuwarsu a kan rashin sanin inda tsohon gwamnansu, Ali Modu Sheriff, ya ke.

SaharaReporters ta wallafa cewa tsohon gwamna Sheriff ya ki amincewa a gwada shi duk da sanin cewa ya yi mu'amala da manyan mutane da cutar covid-19 ta hallaka kwanan nan a jihar Borno.

Mamba a kwamitin yaki da annobar covid-19 a jihar Borno ya ce tsohon gwamnan ya na daga cikin mutanen da aka gano cewa sun yi mu'amala da marigayi Mohammed Goni, tsohon gwamnan Borno, da marigayi Alhaji Kyari Elkanemi, sarkin Bama.

Dukkan manyan mutanen biyu sun mutu ne sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Marigayi Goni da Elkanemi su na daga cikin mutanen da su ka halarci jana'izar mahaifin Sheriff, Galadima Modu Sheriff, wanda ya mutu a makon jiya.

Tsohon gwamna Ali Modu ya yi wa ma'aikatan lafiya wayo, ya sulale ya gudu don kar a gwada shi
Tsohon gwamna Ali Modu Sheriff
Asali: Facebook

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an karya dokokin nesanta da sauran matakan dakile yaduwar annobar covid-19 yayin jana'izar.

DUBA WANNAN: An sake samun kwayar cutar covid-19 a jikin wasu almajirai 14 da Kano ta mayar Kaduna

A cewar rahoton SaharaReporters, Sheriff ya gana da mutanen biyu a tsawon kwanaki uku da aka yi ana zaman makokin rasuwar mahaifinsa a gidansa da ke unguwar GRA a Maiduguri.

Sai dai, wata majiya mai kusanci da tsohon gwamnan ta ce ya tsere zuwa Abuja bayan ya fara matsin lamba daga wurin jami'an cibiyar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) a kan bukatar daukan jininsa domin gudanar da gwaji.

"Mu na mamakin yadda mutum kamarsa zai ke tsoron gwajin cutar covid-19. An kira shi, ba sau daya ba, domin ya zo a gawada shi amma ya ki amsa gayyata. Daga karshe ma ya yaudaresu ya gudu Abuja da wasu tsirarun hadimansa.

"An san cewa ya gana, a lokuta da dama, da tsohon gwamnan jihar Borno, marigayi Goni," a cewar majiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel