Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC

Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC

- Shugaban NCDC, Chikwe Ihekweazu, ya ce al'amura ba za su daidata a Najeriya a cikin shekarar nan ba

- A cewar Ikweazu, ba lallai al'amura su koma daidai a cikin shekarar 2021 ba, sai dai, idan an yi sa'a

- Ihekweazu ya ce matsin da 'yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu tamkar sadaukarwa ce domin gyara gobensu

Chikwe Ihekweazu, shugaban cibiyar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC), ya ce al'amura ba za su dadaita a Najeriya da sauran kasashen duniya a cikin shekarar nan ba, sai dai, watakila zuwa shekara ta gaba.

Da ya ke gabatar da jawabi a wurin wani taro, Ihekweazu ya ce matsin da 'yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu tamkar sadaukarwa ce domin gyara gobensu

Da aka tambaye shi a kan lokacin da al'amura za su koma daidai; a janye dokar nesanta, a daina saka takunkumi da sauran dokokin hana walwala da aka saka saboda annobar covid-19, sai ya ce; "watakila zuwa shekara ta gaba".

"Na san mun shiga wani sabon yanayi da bamu saba da shi ba, haka sauran kasashen duniya su ke fama da irin wannan kalubale da tunanin yaushe al'amura za su koma daidai.

"Maganar gaskiya ita ce, haka za mu cigaba da rayuwa da annobar covid-19 har zuwa cikin wata shekarar, idan ma mun yi sa'a kenan.

"Yanzu kamata ya yi mu fara tunanin yadda za mu yi rayuwa mai tsafta a cikin annobar covid-19, mu na fatan sauye - sauyen da aka zo da su za su taimakawa mutane wajen kare kansu da dakile yaduwar annobar," a cewarsa.

Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC

Chikwe Ihekweazu; Shugaban NCDC
Source: Twitter

Ihekweazu ya ce burinsa shine ganin 'yan Najeriya sun cigaba da kula da tsaftar muhalli da jikinsu hatta bayan annobar covid-19.

"Tsafta ta na da matukar muhimmanci kuma za ta taimaka wajen dakile yaduwar cututtuka ma su yawa," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Gwamnan Bauchi ya amince da amfani da wata kwaya domin maganin cutar covid-19

Shugaban na NCDC ya ce akwai babban kalubale wajen hana taron jama'a, inda ya ce; "zan fi son ganin jama'a su na amfani da fasahar zamani wajen sadarwa. Za mu yi tunanin a kan hanyoyin takaita taron jama'a a kasuwanni, wuraren ibada da wurin taron biki."

Ya zuwa yanzu akwai jimillar mutane 2170 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

Mutane 351 daga cikin adadin sun warke, yayin da annobar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 68 a fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel