COVID-19: SEMA ta bayyana yawan jama'ar da za su samu tallafi a jihar Kano

COVID-19: SEMA ta bayyana yawan jama'ar da za su samu tallafi a jihar Kano

- A kalla gidaje 300,000 ake tsammanin tallafin gwamnatin tarayya da aka tura jihar zai isa

- Kamar yadda hukumar SEMA ta bayyana, tallafin zai ciyar da a kalla mutum miliyan daya a cikin jihar

- Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa manyan motoci 100 dankare da hatsi sun isa jihar Kano

A kalla gidaje 300,000 wadanda ke da mutane 1,000,000 ne za su samu tallafin rage radadi na gwamnatin tarayya a jihar Kano.

Sakataren hukumar al'amuran gaggawa na jihar Kano, SEMA, Dr Saleh Jili ne ya sanar da hakan yayin duba hatsin da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta tura motoci 110 na hatsi don a raba wa mabukatan jihar Kano don rage radadin kullesu da aka yi.

Jili yace gwamnatin jihar tana fatan gidaje 300,000 ne tallafin zai kaiwa a jihar.

Ya kara da cewa, kusan mutum miliyan daya ne ake tsammanin za su mora daga wannan tallafin.

Sakataren SEMA ya jinjinawa gwamnatin tarayya da irin kyautatawar da tayi. Ya kara da cewa hakan zai taka rawar gani wurin taimakawa marasa karfi a jihar.

COVID-19: SEMA ta bayyana yawan jama'ar da za su samu tallafi a jihar Kano
COVID-19: SEMA ta bayyana yawan jama'ar da za su samu tallafi a jihar Kano. Hoto daga sahfin gwamnatin jihar Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

Ya sake jaddada kokarin gwamnatin jihar wajen adalci a raba kayan tallafin ga mabukata.

Hakazalika, Sanusi Ado, shugaban NEMA, ya ce akwai motocin hatsi har 25 da za su shiga jihar Kano din a ranar Alhamis.

Ado ya ce za a adana hatsin a wurare biyar na jihar don a samu sauki rabonsu ga mabukata.

Ya ce tallafin na daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na raba kayan rage radadi ta hannun ma'aikatar noma da kiwo da kuma habaka karkara.

Ado ya ce motocin hatsin za su kammala isowa ne a kwanaki kalilan masu zuwa. Hatsin sun hada da dawa, gero, shinkafa da masara.

"An fitar da hatsin daga ma'adanar abincin kasar nan da ke Dutsinma a jihar Katsina, Lafia a jihar Nasarawa, Minna a jihar Niger, Gusau a jihar Zamfara da kuma Yola a jihar Adamawa," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel