Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano

Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano

Gidauniyar Kwankwasiyya, ta tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta bayyana damuwarta bisa yadda gwamnatin Kano ta yi fatali da kyautar da ta ba ta.

Kimanin kwanaki 10 da suka gabata ne Kwankwaso ya sanar da bai wa gwamnatin jahar Kano kyautar wani asibiti da ya gina mai suna Amana domin a dinga killace masu cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Yabon gwani ya zama dole: Jahohi guda 3 da suka ciri tuta wajen yaki da COVID19 a Najeriya

Asibitin yana nan ne a kan titin Miller, kuma yana cin gado 30 ne, kamar yadda kaakakin dan takarar gwamnan Kano a PDP, Abba Yusuf, Ibrahim Adam ya sanar a ranar 20 ga watan Afrilu.

Sanawar ta kara da cewa asibitin na cike ne da kayan aiki, wadanda Kwankwaso ya sanya a ciki tun zamanin da yake majalisar dattawa.

Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano

Asibtin Amana Hoto: Shafin Confi
Source: Facebook

Amma har yanzu gwamnatin jahar Kano bata amshi wannan kyauta da Kwankwaso ya yi mata ba, kuma bata yi amfani da shi ba, kamar yadda kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana.

Don haka suka zargi Ganduje da yin siyasa da rayukan jama’an Kano ta hanyar kin karbar gudunmuwar da suka bayar domin ceton rayukan Kanawa da lafiyarsu.

“Rayukan miliyoyin mutane ake magana, amma Ganduje yana ta siyasa da gudunmuwar asibitin da gidauniyar Kwankwasiyya ta bayar, ya ki karbar asibitin ne saboda daga wajen Kwankwaso ta fito.” Inji su.

Hakan ya kawo cece kuce a shafin Twitter, inda wani yace: “Idan da gaske ne, lallai abu ya yi muni, na dauka sun warware matsalarsu duba da kimarsu a cikin jama’a.”

Wani kuma ya kare Ganduje kamar haka: “Kwankwasiyya asalin munafukai ne, masu siyasantar da komai, sun san Kano bata bukatar wajen killace mutane, dakunan gwaji kawai jahar Kano take so.”

Amma a wani hira da hadimin Ganduje a kan watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ya yi a daren Alhamis da Japhet Omojuwa a shafin Instagram, ya musanta batun bayar da asibitin.

Yakasai yace a shafukan sadarwar zamani kawai Kwankwaso ya bayar da asibitin, babu wanda ya kawo ma gwamnatin Kano a gwamnatance cewa ga asibiti nan ta yi amfani da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel