Covid-19: 204 sun kamu a ranar Alhamis, Kano ta sha gaban Legas

Covid-19: 204 sun kamu a ranar Alhamis, Kano ta sha gaban Legas

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 204 ne aka tabbatar da cewa kwayar cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa kusan 12:00 na daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

80-Kano

45-Lagos

12-Gombe

9-Bauchi

9-Sokoto

7-Borno

7-Edo

6-Rivers

6-Ogun

4-FCT

4-Akwa Ibom

4-Bayelsa

3-Kaduna

2-Oyo

2-Delta

2-Nasarawa

1-Ondo

1-Kebbi

Alkaluman ma su dauke da kwayar cutar covid-19 da NCDC ta fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, sun nuna cewa jihar Kano, a karo na farko, ta sha gaban jihar Legas a yawan adadin mutanen ta su ka kamu da cutar.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, akwai jimillar mutane 1932 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamnan Bauchi ya amince da amfani da wasu kwayoyi 2 domin maganin cutar covid-19

An sallami mutane 319 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 58.

Alkaluman wadanda annobar covid-19 ta harba da NCDC ke fitarwa a 'yan kwanakin baya bayan nan na nuni da cewa annobar tana kara karfi a arewacin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel