Covid-19: 196 sun kamu a Najeriya, 24 a Kano, 18 a Gombe, 17 a Kaduna da suransu

Covid-19: 196 sun kamu a Najeriya, 24 a Kano, 18 a Gombe, 17 a Kaduna da suransu

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 196 ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa kusan 12:00 na daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

87-Lagos

24-Kano

18-Gombe

17-Kaduna

16- Abuja (FCT)

10-Katsina

8-Sokoto

7-Edo

6-Borno

1-Yobe

1-Ebonyi

1-Adamawa

Legit.ng ta lura cewa an samu karin mutum daya a kan adadin mutane 195 da NCDC ta bayyana cewa sun kamu da kwayar cutar a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu, akwai jimillar mutane 1728 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

DUBA WANNAN: A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatane, 'yan Boko Haram sun mika wuya

An sallami mutane 307 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 51.

Alkaluman ma su kamuwa da NCDC ke fitarwa a 'yan kwanakin nan na nuni da cewa annobar tana kara karfi a arewacin Najeriya.

Kwamishinan lafiya a jihar Borno, Dakta Salihu Kwayabura, ya ce alamu sun nuna cewa kwayar cutar covid-19 ta yadu a tsakanin jama'a. Ya ce akwai bukatar bullo da dabarun binciko wadanda annobar ta harba.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taron da ya saba yi da manema labarai a kullum domin bayar da bayanai a kan halin da ake ciki dangane da yaki da annobar covid-19 a jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel