Akwai yiwuwar yawan mace-macen Kano wani makirci ne na rage yawan musulmi - MURIC

Akwai yiwuwar yawan mace-macen Kano wani makirci ne na rage yawan musulmi - MURIC

- MURIC ta ce rashin bayyana dalilan yawan mace-macen da ake samu a Kano na iya kasancewa wani makirci na rage yawan Musulman Najeriya

- Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya bayyana damuwa kan yaduwar jita-jitar cewa NCDC ta kulle duk ofisoshinta na jihar Kano

- Akintola ya yi zargin cewa martanin da NCDC ta yi kan yawan mace-macen Kano wata kitimurmura ce ta rage yawan mutanen Arewa

Kungiyar MURIC mai kare hakkokin Musulmi a Najeriya, ta yi zargin cewa akwai yiwuwar sakacin da aka yi dangane da yawan mace-mace da ake samu a Kano wani makirci na rage yawan adadin musulmi a kasar nan.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, kungiyar ta yi wannan zargi ne cikin wata sanarwa da jagoranta ya fitar, Ishaq Akintola, a ranar Litinin, 27 ga Afrilun 2020.

Akintola ya yi zargin cewa halin ko in kula da Hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC ta yi dangane da yawan mace-mace da aka samu a jihar Kano wani tuggu ne na rage yawan al'ummar Arewa.

Yana mai cewa: "Shin wannan ko dai wani yunkuri ne na rage yawan 'yan Arewa duba da yadda yankin ya kunshi mafi rinjayen musulmi a kasar nan?"

Shugaban MURIC; Ishaq Akintola

Shugaban MURIC; Ishaq Akintola
Source: UGC

Ya bukaci a gudanar da bincike kan dalilan da suka sanya Hukumar NCDC ta rufe dukkanin ofisoshinta na jihar Kano da kuma rashin wadatattun wuraren gwajin gano masu cuta a yankin Arewa gaba daya.

Babu shakka tun daga mako jiya kawo yanzu, ana ci gaba da samun yawaitar mace-macen mutane musamman dattawa a Kano da suka hada da manyan ma'aikatan gwamnati, malaman jami'a wanda wasunsu sun kai matakin Farfesa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta gargadi gwamnoni a kan gasar adadin masu cutar korona a jihohinsu

Ganin irin yawan mace-macen da ake samu a jihar, ya sanya tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari wasika, ya na rokon a kawowa jihar dauki.

A cikin wasikar da ya aikewa shugaban kasar, Sanata Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta ceton rayukan al'ummar jihar Kano.

Ana zargin cewa akalla mutane 600 sun mutu a Kano a makon da ya gabata kadai.

Ko a ranar Asabar da ta gabata, fiye da mashahuran mutane 10 'yan asalin jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya. Cikin su akwai editan babban kamfanin jaridar nan ta Triumph, Musa Tijjani.

Sauran mashahuran mutanen da ajali ya cimma a ranar Asabar din sun hadar da; Farfesa Ibrahim Ayagi, Dr. Musa Gwarzo, Dahiru Rabiu, Adamu Dala, Salisu Lado, Shamsiyya Mustapha, Nene Umma, Garba Fagge, Nasiru Bichi, Farfesa Aliyu Umar Dikko da kuma Aminu Yahaya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata, an binne gawawwakin kimanin mutane 150 a cikin birnin Kano sanadiyar wata bakuwar cutar, lamarin da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya na da matukar tsorataswa.

Da dama dai na zargin cewa cutar korona ce ke hallaka mutane a Kanon yayin da wasu ke alakanta mace-macen da cututtuka irinsu hawan jini, sankarau, zazzabin cizon sauro, ciwon sukari da sauransu.

Mun jin cewa Shugaban Najeriya ya bayyana damuwa kan mace-macen da aka samu a jihar Kano da ke Arewacin kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar kan annobar cutar korona a ranar Litinin da daddare.

Shugaban ya ce ya aika da tawaga domin gudanar da bincike tare da kulle jihar na tsawon mako biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel