Yawan mace-mace ya jefa al'ummar Kano cikin firgici
Mun samu rahoton cewa a ranar Lahadi wasu manyan mutane biyu a jihar Kano sun rasa rayukansu sanadiyar wata bakuwar cuta da hakan ya sake jefa tsoro a zukatan al'umma.
Mutanen biyu wadanda mai yankan kauna ta katsewa hanzari a baya-bayan nan sun hadar da tsohon kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Aminu Yahaya, da kuma wani farfesan nazarin aikin jarida na jami'ar Bayero, Farfesa Balarabe Maikaba.
A ranar Asabar kadai, fiye da mashahuran mutane 10 'yan asalin jihar Kano suka riga mu gidan gaskiya. A cikin su akwai editan babban kamfanin jaridar nan naTriumph, Musa Tijjani.
Sauran mashahuran mutanen da ajali ya cimma a ranar Asabar din sun hadar da; Farfesa Ibrahim Ayagi, Dr. Musa Gwarzo, Dahiru Rabiu, Adamu Dala, Salisu Lado, Shamsiyya Mustapha, Nene Umma, Garba Fagge, Nasiru Bichi, Farfesa Aliyu Umar Dikko da kuma Aminu Yahaya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata, an binne gawawwakin kimanin mutane 150 a cikin birnin Kano sanadiyar wata bakuwar cutar, lamarin da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya ci tura.
Babu shakka a baya-bayan nan an ci gaba da samun yawaitar mace-mace mutane musamman dattawa a Kano da suka hada da manyan malaman jami'a da wasunsun sun kai matakin Farfesa.

Asali: UGC
Sabanin tabbacin da gwamnati ta bayar na shawo kan wannan annoba, har yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa mutuwa na ci gaba da yin aringizo a birnin Kanon Dabo.
Gwamnatin Kano ta bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu tare da basu tabbacin cewa nan bada jimawa ba gwamnati za ta gano bakin zaren.
KARANTA KUMA: Sauran kiris mu wajabta amfani da takunkumin rufe fuska a Kano - Ganduje
Furucin rarrashi gami da kwantar da hankalin al'umma na ranar Lahadi, ya fito ne daga bakin Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba.
A cewar Sabitu Shaibu, mataimakin shugaban kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kano, ya ce adadin mutanen da su ka mutu a Kano ya kai 640, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Da dama dai na zargin cewa annobar cutar korona ce ke hallaka mutane a Kano. Sai dai, kamar yadda kwamishinan ya bayyana, mutane na mutuwa ne daga cututtuka irinsu hawan jini, zazzabin cizon sauro, ciwon sukari da sauransu.
A nasa jawaban mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa yawan mace-macen da ake yi a Kano ba ta nasaba da annobar corona sabanin yadda wasu ke ikirari.
Madogarar wannan furuci da mai martaba ya yi a ranar Lahadin, ba ta wuce shaidar da Ma'aikatar Lafiyar jihar ta yi ba na rashin alakanta yawaitar mace-macen da cutar corona.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng