Sarkin Kano ya yi magana a kan yawaitar mutuwar jama'a a masarautarsa

Sarkin Kano ya yi magana a kan yawaitar mutuwar jama'a a masarautarsa

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa ba annobar covid-19 ce ke hallaka mutane a masarautarsa ba, kamar yadda wasu su ke zargi.

A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, Sarkin ya ce ma'aikatar lafiya ta jiha ta sanar da fadarsa cewa asarar dumbin rayukan da ake yi, ba sanadiyyar barkewar annobar cutar covid-19 bane.

Ya yi addu'ar Allah ya ji kan wadanda su ka mutu tare da yi wa marasa lafiya fatan samun sauki.

Da ya ke magana a kan annobar cutar covid-19, sarki Aminu ya yi kira ga mazauna Kano da su yi aiki da shawarwarin da hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta bayar a kan dakilye yaduwar covid-19.

Bayan ya yi sallama ga jama'a, sarki Aminu ya ce; "mu na son sanar da jama'a cewa ma'aikatar lafiya ta aiko mana da rahoto a kan yanayin da ake ciki dangane da barkewar annobar covid-19 a jihar Kano.

"Rahoton yana da matukar muhimmanci, saboda ya tabbatar mana da cewa cutar covid-19 gaskiya ce tunda ga shi an tabbatar da samun mutane 73 ma su dauke da ita a Kano.

"A dangane da haka, ya zama wajibi garemu mu yi muku tuni a kan muhimmancin bin shawarwarin masana da kwararru a bangaren kiwon lafiya.

Sarkin Kano ya yi magana a kan yawaitar mutuwar jama'a a masarautarsa

Sarkin Kano
Source: Twitter

"Ku guji wurare ma su cunkoson jama, a ke amfani da takunkumi tare da yawaita wanke hannu da sabulu.

"Mu na kira gareku da ku daina kyarar wadanda annobar cutar ta harba, a guji yada labaran karya da kan iya firgita jama'a.

DUBA WANNAN: Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

"Ina kira gareku da ku saka ido a kan 'ya'yanku don tabbatar da cewa basu cigaba da buga kwallo a cikin lunguna ba.

"Kazalika, ma'aikatar lafiya ta ba mu tabbacin cewa ba annobar cutar covid-19 ce ke hallaka mutane a Kano ba.

"Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan duk wanda su ka rasa wani nasu, ina kira ga jama'a su kwantar da hankalinsu tare da cigaba da neman taimakon Allah.

"Marasa lafiya Allah ya basu lafiya, Allah ya cigaba da karemu, ya ba mu zaman lafiya da yalwar arziki," a cewar jawabin sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel