Yadda annobar covid-19 ta hallaka mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya

Yadda annobar covid-19 ta hallaka mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya

Annobar cutar covid-19 ta hallaka Francis Bissong, mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya mai kula da sashen binciken manyan laifuka, a jihar Edo.

Bissong, babban jami'in dan sanda, ya mutu ne a gidansa da ke birnin Benin a ranar Talatar da ta gabata.

Duk da kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Patrick Okundia, ya sanar da mutuwar Bissong, amma bai yi karin bayani a kan mutuwar ba.

Paul Yakadi, mataimakin shugaban rundunar 'yan sanda na shiyya ta 5 da ke Benin, ya fitar da cikakken bayani a kan mutuwar Bissong, wanda ya bayyana da 'hazikin dan sanda'.

Yakadi ya ce a ranar 9 ga watan Afrilu ne marigayi Bissong ya yi bulaguro zuwa Akure, babban birnin jihar Ondo, domin yin bikin ista tare da iyalinsa.

Ya dawo Benin bayan ya shafe kwanaki biyar a Akure, kuma bayan dawowarsa ne ya yi korafin cewa yana fama da zazzabi mai zafi, lamarin da ya sa shi killace kansa.

Yadda annobar covid-19 ta hallaka mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya

Marigayi Bissong
Source: Twitter

"An dauki jininsa a ranar 18 ga watan Afrilu domin gudanar da gwaji, inda kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar covid-19," a cewar jawabin da Yakadi ya fitar.

Jawabin Yakadi ya cigaba da cewa; "nan da nan muka tuntubi ma'aikatan hukumar shawo kan cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) domin su zo su dauke shi zuwa cibiyar killacewa, amma kafin su zo ya mutu, sai gawarsa su ka zo su ka samu."

DUBA WANNAN: Jihohi 6 da aka samu karin mutane 23 da annobar covid-19 ta harba

Kazalika, Yakadi ya yi watsi da rahotannin da suka bayyana cewa Bissong ya mutu ne a wani asibitin rundunar 'yan sanda da ke Benin.

"Domin kore duk wani shakku, zan sake maimaita cewa marigayi Bissong ya mutu ne a gidansa da ke rukunin gidajen manyan jami'an 'yan sanda da ke daf da hedikwatar 'yan sanda shiyya ta 5 da ke birnin Benin," a cewarsa.

Dukkan wasu jami'an 'yan sanda da suka yi mu'amala da marigayi Bissong sun killace kansu, yayin da aka saka maigadinsa, direba da sauran hadimasa a karkashin kulawa ta musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel