Mutum 6 sun warke daga cutar covid-19 a jihar Kaduna

Mutum 6 sun warke daga cutar covid-19 a jihar Kaduna

An sallami karin wasu mutane 6 da su ka warke daga cutar covid-19 a Kaduna, a cewar kwamishinar lafiya ta jihar, Amina Mohammed Baloni.

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

"An sallami Mallam Nasir El-Rufa'i, mutum na farko da ya kamu da cutar covid-19 a Kaduna, a ranar 22 ga watan Afrilu, 2020, bayan sakamakon gwaji guda biyu da aka sake yi masa sun nuna ya warke.

"kafin warkewarsa, an sallami mutum biyar da ke dauke da kwayar cutar a cikin sati daya. An fara sallamar wanda su ka warke daga ranar 14 ga watan Afrilu," a cewar Baloni.

Kazalika, ta bayyana damuwarta a kan sake samun mai dauke da kwayar cutar a Kaduna, inda ta bayyana cewa ya zuwa ranar Asabar, adadin ma su dauke da kwayar cutar a jihar ya zama mutum hudu.

Baloni ta ce ana gudanar da bincike tare da bin sahun mutanen da sabon mai dauke da kwayar cutar ya yi mu'amala da su kafin a gano yana dauke da ita.

Ta ce za a gwada mutanen tare da killacesu da kuma sa-ido a kansu.

A ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu ne rahotanni su ka bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i ya warke daga cutar coronavirus.

El-Rufa'i ya wallafa a shafinsa na sada zumunta (tuwita) cewa ya warke daga cutar covid-19 bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar yanzu.

Mutum 6 sun warke daga cutar covid-19 a jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

A cikin wani jawabi da ya fitar bayan an sallame shi, El-Rufa'i ya ce akwai bukatar sadaukarwa da inganta tsaftar jiki da ta muhalli tare da kauracewa taron jama'a domin samun galaba a kan annobar cutar covid-19.

DUBA WANNAN: Covid-19: Kura-kurai 7 da 'yan Najeriya ke tafkawa wajen amfani da takunkumi

"Zan rufe jawabina da sanar da mutanen jihar Kaduna cewa na zo da sabuwar dokar bukatar jama'a su saka takunkumin fuska yayin da za su fita daga gidajensu a kan kowanne dalili.

"Gwamnati za ta samar da takunkumin rufe fuska ga talakawa da ma su karamin karfi. Hakan zai taimaka wajen kare kowa da kowa da kuma dakile yaduwar cutar," a cewarsa.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin kauracewa taron jama'ar da yawansu ya kai 10, zama a gida tare da yawan wanke hannu da sabulu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel