Covid-19: Ganduje ya aika wa masu dakunan gwaji na jihar da sakon gaggawa

Covid-19: Ganduje ya aika wa masu dakunan gwaji na jihar da sakon gaggawa

- Cibiyar kula da ma'aikatun lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano ta bada sanarwar cewa asibitoci 300 masu zaman kansu a jihar ne za su iya aiki

- Cibiyar ta umarcin dukkan dakunan gwaji masu zaman kansu na jihar da su gaggauta rufewa tare da daina aiki

- Kamar yadda Dr Usman Eti ya ce, asibitocin masu zaman kansu da suka mallaki kayayyakin kariya na ma'aikatan lafiya ne kadai za su iya killacewa

Cibiyar kula da ma'aikatun lafiya ta kudi ta jihar Kano ta bada sanarwar cewa asibitoci 300 na kudi a jihar Kano ne za su iya aiki amma iyakar abinda suka yi rijista.

Cibiyar ta shawarci dakunan gwaji da ke jihar da su daina aiki na wannan lokacin. Cibiyar ta kara da jan kunne asibitocin kudin cewa za ta iya rufe su matukar basu da kayan kariya na ma'aikatan lafiya.

Sakataren cibiyar, Dr Usman Eti ya sanar da jaridar The Punch a ranar Juma'a cewa wannan dokar na daga cikin umarnin gwamnatin jihar ga masu cibiyoyin lafiya na kudi.

Hakan ce hanya daya da za ta takaita yaduwar cutar ga ma'aikatan lafiya na cibiyoyi masu zaman kansu.

Covid-19: Ganduje ya aika wa masu dakunan gwaji na jihar da sakon gaggawa

Covid-19: Ganduje ya aika wa masu dakunan gwaji na jihar da sakon gaggawa
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mahaifiyar ministan Ilimi, Adamu Adamu ta rasu

Eti ya ce, "An kiyaye wannan umarnin ne tun daga kungiyar likitoci ta Najeriya, kungiyar ma'aikatan jinya da ungo-zoma da kuma kungiyar masu hada magani ta kasa.

"Duk cibiyoyin killacewa masu zaman kansu da suka mallaki kayayyakin kariya na ma'aikatan lafiya za su iya aiki.

"Ba mu fatan abinda ya faru a jihar Legas ya maimaita kansa a nan. Dole ne mu kiyaye."

Ya kara da cewa, "An shawarci dukkan dakunan gwaji masu zaman kansu da su rufe tare da daina aiki."

Kamar yadda yace, cibiyar tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da kwamitin yaki da cutar na jihar za su saka ido a kan hakan.

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa a ranar Alhamis ta ce mutum 73 ne suke dauke da cutar COVID-19 a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel