Wani Gwamna ya yi umurnin suburbudan duk mutumin da ya fito babu takunkumin fuska a jaharsa

Wani Gwamna ya yi umurnin suburbudan duk mutumin da ya fito babu takunkumin fuska a jaharsa

Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, ya bukaci jami’an kananan hukuma da su yi wa mazauna jahar da suka fito babu takunkumin fuska dukan tsiya.

Umahi ya ce yana da matukar muhimmanci mutane su dunga amfani da takunkumin fuska domin hana yaduwar COVID-19 a jahar.

Gwamnan ya bayyana hakan a yayin da ya ke jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a ranar Laraba, a Abakaliki, babbar birnin jahar, jaridar TheCable ta ruwaito.

Ba a samu ko mutum da ke da COVID-19 ba a Ebonyi.

Wani Gwamna ya yiumurnin suburbudan duk mutumin da ya fito babu takunkumin fuska a jaharsa
Wani Gwamna ya yiumurnin suburbudan duk mutumin da ya fito babu takunkumin fuska a jaharsa
Asali: Facebook

“Bari na sake gargadin cewa duk wanda bai sa takunkumin fuska ba a jahar Ebonyi, kada ya fito bainar jama’a,” in ji gwamnan.

“Idan baka sa takunkumin fuska ba sannan ka fito waje, Ina umurtan Shugabannin kananan hukumomi da su yi amfani da jami’ansu wajen tursasa bin dokar, wanda matakin shine duka da bulala.

“Idan ba ka sa takunkumin fuska ba, za ka sha duka, ko kai wanene. Idan kai babban mutum ne kuma za ka fita waje sannan ba ka da takunkumin fuska, toh za ka jawo wa kanka rigima kuma dokar a bayyane ta ke.

“Mun kuma ta jadaddawa, har babban kwamanda na ya yi gargadin cewa ya zama dole a ci gaba da bin oda na rufe hanyoyi.

“Ya zama dole yan sanda su rufe iyakar jahar na farko, sannan sojoji su ba da yar tazara sannan su toshe hanyar, sannan sauran hukumomin tsaro su toshe nasu, a yanzu kallo ya koma ga makwabta ne.”

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya rufe masallatan Juma’a, ya hana taron tafsiri

A ranar Laraba, Umahi ya hana wasu yan jarida biyu daukar rahoto a kan ayyukan jahar kan “rubuta rahotanni marasa kyau game da jahar”.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya ce dole jama'a su yi biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar annobar.

El-Rufa'i ya ce akwai bukatar sadaukarwa da inganta tsaftar jiki da ta muhalli tare da kauracewa taron jama'a domin samun galaba a kan annobar cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng