Yanzu-yanzu: Cutar Covid-19 ta bulla jihar Filato

Yanzu-yanzu: Cutar Covid-19 ta bulla jihar Filato

Gwamnatin jihar Filato ta tabbatar da bullar cutar Covid-19 a karo na farko.

Wacce ta kawo cutar jihar mace ce wacce ake zargin ta kwaso kwayar cutar daga jihar Kano inda ta kai ziyara duk da dokar hana zirga-zirgar da aka kafa a jihar.

"Eh, mun samu bullar cutar a karon farko a jihar Filato. An samu kwayar cutar ne daga jikin wata mata wacce ta dawo daga jihar Kano.

"Babu bukatar a tada hankali, a halin yanzu tana daya daga cibiyar killacewa ta jihar.

"Amma tambaya ta farko da za mu yi shine ta yaya har matar ta fita daga jihar Filato ta je Kano kuma ta dawo duk da iyakokinmu a rufe suke," wani likita ya sanar da jaridar SaharaReporters.

KU KARANTA: COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki

Kwamitin shugaban kasa na yakar cutar Covid-19 ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja a jiya yayin jawabi ga kwamitin.

Ya ce: "Halin da jihar Kano ke ciki abin tada hankali ne. Kwamitin na ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar don shawo kan lamarin.

"Kwamitin ya gano cewa ana ci gaba da samun masu cutar a kasar nan. Wannan kuwa ya danganta ne da yadda aka fadada wuraren gwajin."

Mustapha ya kara da cewa, ganin yadda lamarin ya sake yawaita, sun sauya sabbin tsarin gwaji don yanzu gida-gida ake bi don yin gwajin a jihohin Legas da Abuja.

Kamar yadda yace, gwaji, tantancewa, killacewa da kula da masu cutar ya zama dole in har ana bukatar takaita yawan masu kamuwa da cutar.

Ya mika godiyarsa ga sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a kasar nan a kan kwamitin fatawa ta gaggawa da ya kafa.

Ta hakan ne aka samu wadanda suka wayar da kai ga al'umma ta yadda za a yi azumin watan Ramadan duk da dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel